✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NEMA za ta ziyarci kananan hukumomin da Boko Haram ta yi barna

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta ce nan bada dadewa ba jami’anta da hadin gwiwar jami’an tsaro, za su fara ziyarar kananan…

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta ce nan bada dadewa ba jami’anta da hadin gwiwar jami’an tsaro, za su fara ziyarar kananan hukumomin da kungiyar Boko Haram ta yi wa barna a Jihar Borno, don ganowa tare da tantance yadda hukumar za ta tallafaw a al’ummomin da abin ya shafa.

Daraktan Bincike da Bada Agaji na Hukumar ta kasa Iya Kwamanda Charles Otekgbade, ya fadi haka a lokacin da yake mika wa gwamnatin jihar kayayyakin masarufi don agaza wa ’yan gudun hijira da ke sansanonin garin Maiduguri.
Kwamanda Otekbade, ya ce aikinsu shi ne bayar da agajin gaggawa ga mutanen da wani bala’i ya shafa aukawa, kuma ba su tsaya a nan ba suna shiga wuraren da barna ta auku su kiyasta irin taimakon da za su iya yi wa al’umma, “Don haka nan ba da dadewa ba za mu fara rangadin kananan hukumomin da Boko Haram suka lalata a Borno, domin bincike da agaza wa al’ummomin garuruwan da abin ya shafa,” inji shi.
Kwamanda Charles Otekbade, ya kara da cewa, hukumar kamar yadda ta saba ta kawo wa ’yan gudun hijirar taimakon abinci da kayayyakin masarufi ta yadda za su samu saukin rayuwa, kuma za ta gajiya ba wajen samar musu da ababen more rayuwa har zuwa ranar komawarsu gidajensu, koda gwamnatocin jihohi suna yin nasu kokarin.
Da yake mayar da jawabi a madadin gwamnatin jihar, Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Zanna Umar Mustapha, ya zayyano nau’o’in barnar da ’yan Boko Haramun suka yi ne na kone-konen gine-gine da barnata dukiyoyi, baya ga kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a kananan hukumomi kusan 20 na jihar.
Ya ce akwai sansanonin ’yan gudun hijira 15 a cikin garin Maiduguri kadai, kuma akwai sama da mutum miliyan daya da aka raba su da muhallansu, kuma duk da gwamnatin jihar ta kafa kwamitin zagayawa da tallafa wa wadanda abin ya shafa, har yanzu suna bukatar taimakon Gwamnatin Tarayya don ci gaba da tallafa wa mutanen tare da sake tsugunar da su a muhallansu.