✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta tara N5bn a 2021

Adadin kudaden dai ya haura na 2020 sosai

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce a shekara ta 2021 kadai, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta tara Naira biliyan biyar a matsayin kudaden shiga daga fasinjoji.

Wannan dai na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar ta fitar a Abuja ranar Laraba.

NBS ta ce an samu karin kaso fiye da 226 cikin 100 idan aka kwatanta da kudin shigar da hukumar ta tara a 2020 wanda bai wucce Naira biliyan daya da rabi ba.

Hukumar ta kuma ce fiye da fasinjoji miliyan biyu ne suka yi mafani da jirgin kasan a 2021, idan aka kwatanta da miliyan dayan da suka yi mafani da shi a 2020, za a ga an samu karin kaso 166 ke nan na adadin.

Kazalika rahotan ya kuma bayyana yadda aka samu karin kudaden shiga ta kayan masurufi a 2021 da ya kai na Naira miliyan 317, wanda ya dara kaso 12 cikin 100, idan aka kwatanta da Naira miliyan 281 da aka samu a 2020.