✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar yaki da cin hanci ta gargadi ’yan kasuwa a Kano

Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta bai wa ’yan kasuwar da suke boye abinci da sauran kayan masarufi da nufin kara farashi…

Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta bai wa ’yan kasuwar da suke boye abinci da sauran kayan masarufi da nufin kara farashi wa’adin sa’o’i 24 da su fitar da kayan ko kuma su tafka asara.

Hukumar ta kuma umarci wadanda suke tsawwala farashin kayayyaki ba bisa ka’ida ba su sauke farashi ko kuma su fuskanci fushinta.

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a Kano inda ya ce sun gano wasu ’yan kasuwa suna amfani da matsin da aka shiga dalilin dokar zaman gida saboda yaki da cutar coronavirus suna kara farashin kayayyaki.

Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Rimingado yana cewa hakan yana barazana ga zaman lafiya a jihar da kokarin da gwamnati ke yi na dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

“Karin farashi ba bisa ka’ida ba laifi ne a karkashin kundin dokar yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar Kano.

“Hakan yana iya barazana ga zaman lafiyar jihar, ganin cewa malaman addini da dama sun yi tsokaci a kan hakan a tafsiransu na watan Ramadan,” inji shi.

Ya ce hukumar za ta yi amfani da bayanan da ta samu na sirri wajen nemo wadanda suke aikata hakan sannan ya yi nuni da cewa sashe na 39 na dokar yaki da cin hanci da sauraren koke-koken jama’a  ya bai wa hukumar damar kwace kayayyakin da aka boye.

Ya kara da cewa kasuwannin da hukumar take shirin kai samame sun hada da kasuwar Singa; Dawanau, Hadejia Road, Bello Road, Malam Kato, Gezawa da kasuwar Sharada.

Rimingado ya kuma ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da samamen da hukumar za ta fara saboda hauhawar farashin kayayyakin na kara takura al’ummar jihar.

Idan za a iya tunawa dai Gwamna Ganduje ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan kasuwa suka kara farashin kayayyaki da sama da kashi 100 a jihar.