✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumomin yaki da rashawa su sa ido a kan bankunan —Lawan

Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da fasahar zamani wurin tattara kudaden haraji da dakile karkatar da kudaden gwamnati. Shugaban Majalisar, Sanata…

Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da fasahar zamani wurin tattara kudaden haraji da dakile karkatar da kudaden gwamnati.

Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya yi kiran a taron yaye daliban makarantar horas da kwararru kan binciken kwakwaf ta Najeriya ranar Alhamis.

Sanata Lawan, ya ce yawancin kasashen duniya sun toshe hanyoyin almundahana ta hanyar amfani da fasahar tabbatar da sanya idanu kan al’amuran gudanarwan yau da kullum.

Lawan ya ce: “A Majalisar Tarayya mun gano cewa sau tari hukumomi na tattara kudaden haraji amma ba a shigar da su asusun gwamnati yadda ya kamata.

“Muna da yakinin idan muka yi amfani da hanyoyin zamani na tattara kudaden haraji za mu zarce yadda muke a halin yanzu ta fuskar haraji.

“Wannan dalilin ne ya sa Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS) ke samun cikakken goyon bayan Majalisar Tarayya wurin amfani da hanyoyin kimiyya wurin tattara haraji da dakile zurarewar kudade ta barauniyar hanya”.

Shugaban Majalisar ya kuma bukaci hukumomin yaki da rashawa su sanya idanu kan yadda bankunan kasuwanci ke gudanar da ayyukansu a fadin Najeriya.

“Ba ma’aikatu da hukumomin gwamnati kadai ke da irin wadannan dabi’u ba harda masu zaman kansu, don haka lallai akwai bukatar hukumomin yaki da rashawa su sanya idanu a kansu”, inji Lawan.