✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahim Ahmad: Makahon da ke saka kayan adon daki

Duk da makantarsa, ya rungumi sana'ar saka

Masu iya magana na cewa babu nakasasshe sai kasasshe. Wannan ga alama shi ne dalilin da ya karfafa gwiwar Malam Ibrahim Ahmad, wani makaho dan asalin Jihar Kano, yin sana’ar saka. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce yakan kai kayan da ya saka zuwa jihohi da dama da kuma Abuja domin ya sayar. Haka kuma, an taba gayyatarsa don ya koya wa masu ido sana’ar tasa:

Mene ne tarihinka a takaice?

To, sunana Ibrahim Ahmad, ni haifaffen kauyen Rubun ne da ke mazabar Fanda a karamar Hukumar Albasu a Jihar Kano, kuma yanzu ina da shekara 33. Na sami matsalar gani ne tun ina da shekara biyar a duniya. Amma duk da haka, na yi makarantar allo, inda na yi sauka biyu, kodayake ban samu yin makarantar boko ba. Bayan na yi aure sai na nemi sana’ar yi.

Yaya wannan sana’ar taka take?

Da farko na fara sana’ar jagwal, wato saye da sayar da waya. Ta sanadin haka ne da na je Jihar Nasarawa sai na hadu da wani da yake sana’ar saka, sai na koya a wajensa.

Dama tun farko ba ni da ra’ayin yin bara, sai dai idan ta zama dole. Wannan ne ya sa na koya. Da na ga na iya, kuma na fahimci wannan sana’ar ta fiye min sayar da waya, sai na kyale waccan na rungumi wannan.

Yaushe ka fara saka?

Yanzu na kai shekara shida da farawa. Kuma alhamdulillahi tun daga lokacin ban tsaya ba, da ita nake ci nake sha.

A wane gari ka fara sana’ar?

Na fara a wani gari da ake kira Asin a kusa da Marabar Nyanya a Jihar Nasarawa. Dama nakan zauna a can, idan na kwana biyu in koma gida. Daga nan nakan karasa har Abuja da Kaduna. Har Allah Ya sa mutane suka fara gani suna sha’awa. A lokacin ba ni da takamaiman wurin zama, zagayawa nake yi wajewaje.

Ibrahim Ahmad, makaho da yake saka kayan adon daki
Ibrahim Ahmad, makaho da yake saka kayan adon daki

A haka sai Allah Ya hada ni da wani bawan Allah da ya kama min wajen da nake zama. Da kudin shagon ya kare (Naira 70,000) tunda ba zan iya sake biya ba, sai na je tashar jirgin kasa ta Kaduna da ke Rigasa.

A lokacin nakan baje-kolin wadanda na kammala da wadanda nake yi, saboda wani idan bai ga ina yi ba, ba zai yarda ni nake yi ba, zai dauka ko sarowa nake yi na sayar.

Sai na ga nan din ya fi. Kafin in koma can, nakan iya yin wata daya ban sayar da ko guda daya ba, sai dai in ranci abin da zan ci abinci, idan na sayar in biya. Amma tun lokacin da na je tashar da wahala in yi mako ban sayar ba, wani lokacin wani ma idan ya zo yakan sayi uku ko hudu.

Gaskiya ba na rasa abin da zan ci abinci, saboda wani idan ya ga abin da nake yi ko da ba zai yi amfani da shi ba yakan saya don karfafa min gwiwa.

Galibi mata sun fi shahara da wannan sana’a. Me ya sa ka zabe ta?

To asali ma gaskiya ba ni ake koya wa wannan sana’a ba. Akwai wanda ake koya wa, sai nake cewa ni kuwa da ni ake koya wa wannan aikin da zan iya, saboda ban taba tunanin akwai abin da za a koya min in kasa yi ba.

Da wanda ake koya wa ya kasa iyawa, sai aka ba ni kayan aikin da yake amfani da su aka koya min, sai na ga ya yi. Sai na dauka na fita da shi. Cikin ikon Allah ranar da na fita da shi na sayar. Sai na ce to ai ni alhamdulillahi na samu sana’a. Na zo na ba su kudin kayan aikin, sannan na samu nawa.

To gaskiya wannan shi ne ya burge ni. Kuma a baya kafin in fara wannan sana’a, idan na je wani wajen, ko tambaya zan yi sai ka ga wani ma ba zai kula ni ba, sai a yi tunanin ko bara zan yi.

Amma tunda na fara wannan sana’a na hadu da mutane daban-daban, kuma a duk inda aka gan ni da wadannan kayayyaki an san sana’a nake yi, ko tambaya na yi nan da nan za a nuna min.

Hakan sai ya kara karfafa min gwiwa na ga ya kamata in dada rike sana’ar da gaske.

Mutane da yawa za su yi mamakin a matsayinka na mai larurar gani kake yin sana’ar masu idanu. Yaya kake yin sakar?

Ai abin lissafi ne. Kowanne akwai adadin duwatsun da za ka jera daidai gwargwado. Abu ne da ake yi da hannu, ba dole sai ido ya gani ba. Abin da ake bukata ido ya gani kawai shi ne kofar da za a sa zaren. Ita kuma kofar da ake amfani da zaren tana da karfi, kuma da na laluba nakan gane ta.

Don yanzu haka ma masu idanun da nake koyawa kafin su zura daya, ni na zura da yawa na yi musu nisa. Kuma tun tasowa ta na taso ne a cikin mutane ne masu gani, kuma gidanmu babban gida ne, duk irin giggiwar da yara suke yi ban yarda akwai wacce ba zan iya yi ba.

Ta yaya kake iya bambance launukan duwatsun ganin cewa sun bambanta?

Dama idan na je saye nakan ce ga launin da nake so a ba ni. Idan kuma wani ne ya sa na yi masa zan sayo gwargwadon launukan da yake bukata. Idan na saya na zo gida zan zauna a ware min su, sai in zuba a leda daban-daban kuma in yi musu shaida ta yadda idan na taba zan gane su.

Saboda wani lokacin zan tashi yin aikin babu wanda zai duba min su ko kuma da daddare ma idan na tashi zan yi, maimakon in takura wa wani in tashe shi daga barci, sai kawai in dauki abina in ci gaba da yi.

Wadanne nasarori ka samu sanadin wannan sana’a?

To suna da yawa gaskiya. Akwai wadanda suka taba taimaka min kamar wani lokaci da na dade ban sayar da kayan ba ga bashi ya fara yi min katutu, sai na samu ta dalilinsu na biya basussukan.

Akwai wani bawan Allah shi ma da ya gan ni ya taimaka min, watakila da ba don ya gan ni da wannan sana’ar ba, ba lallai ne ya taimaka min ba. Sannan babban taimakon da ba zan manta da shi ba, shi ne ana dab da za a kai harin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja, akwai wata mata da ta gan ni a tashar ina yi, sai ta ce na burge ta, ta sayi guda daya.

Amma ta ce akwai dalibai da take koya wa sana’o’i a Kano, sai ta dauke ni in koya musu na tsawon mako daya. Kudin da ta biya suna da yawa, domin kwana biyu bayan ranar da aka yaye daliban aka yi min haihuwar tagwaye.

Idan da ba don abin da ta ba ni ba, da ban san yadda zan yi ba. A cikin abin da ta ba ni na yi hidimar suna da su na kuma sayi karin kayan aiki. Ranar da na koma, ranar wata Litinin aka kai harin jirgin kasan nan. Da ba don wannan tallafin ba da ban san yadda zan yi wannan hidimar ba.

Gaskiya alhamdulillahi, a cikin wannan sana’ar ni da iyalaina muke ci muke sha, har ma na samu in biya kudin hayar inda nake zama. Kamar nawa kake sayar da kowane guda daya idan ka saka? Idan ban sa fulawa a jiki ba, nakan sayar da shi Naira 4,000, amma idan na sa fulawa, nakan sayar da shi Naira 5,000. Amma akwai wanda ya fi wannan girma akwai kuma wanda bai kai shi ba.

Wadanne garuruwa kake kai kayan ka sayar?

Nakan kai su Abuja da Kaduna. Amma da Allah Ya taimake ni na samu waje na dindindin a wannan tashar jiragen kasan, sai na zauna waje daya, na daina zagayawa. Sai dai tun bayan faruwar harin guda daya na sake sayarwa, shi ma wani ne ya saya kuma sai da na yi masa ragi shi ma.

Amma yanzu ina zuwa Kano da Dutse da Wudil ina zazzagayawa, idan wani ya gani yana so ya saya.

Wane buri kake da shi a wannan sana’ar yanzu?

Gaskiya babban burina yanzu a wannnan sana’ar shi ne in ga na rike kaina da iyalina, yarana su ci gaba da karatu, sannan duk wata hidima da za ta taso min in fi karfinta.