✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ICPC da DSS sun hada kai don yakar rashawa a Sakkwato

Hukumomin biyu sun bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da jagororin ICPC suka kai ofishin DSS na jihar.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da sauran Ayyukan Almundahana ta Kasa (ICPC), ta yi hadin gwiwa da Hukumar tsaro ta DSS domin fatattakar cin hanci a Jihar Sakkwato.

Hukumomin biyu sun bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da jagororin ICPC suka kai ofishin DSS na jihar.

Shugaban ICPC reshen jihar, Dokta Garba Idris ya ce ziyarar guda ce daga yunkurin Hukumar na yaukaka alaka tsakaninsu da DSS domin kawo karshen cin hanci da rashawa a jihar.

“Mun zo ne domin neman hadin kanku, mu kuma yi aiki tare domin cim-ma manufa guda.

“Haka kuma a matsayinmu na Hukuma mun yi imanin cewa ba za mu iya yakar cin hanci ba mu kadai, dole sai da taimakonku,” in ji shi.

A nasa bangaren, Daraktan DSS na jihar, Yahaya Hassan, ya ce wannan yunkuri na ICPC abin a yaba ne, kuma su ma a shirye suke domin aiki tare da su domin cimma makuasudin samar da su.

“DSS da ICPC na da manufa guda, don haka hada gwiwa tsakaninmu abu ne da zai haifar da kyakkyawan sakamako a jihar.

“Rashawa ne tushen duk kalubalen da muke fuskanta, don haka da zarar mun kawo karshensu, sauran laifuka za su zamo tarihi gaba daya.

“Bugu da kari, idan muka hada hannu wajen yaki da cin hanci da rashawa, zai fi zamowa mafi alheri ga makomar kasarmu,” in ji shi.