✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ICPC ta gano bankin da ya boye sabbin kudi na Naira miliyan 285 a Abuja

An gano yadda bankin ya boye miliyan 285 a rumbun ajiyarsa.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta gano yadda bankin Sterling ya boye Naira miliyan 258 na sabbin kudi a Abuja.

A cewar ICPC, ta gano hakan ne a kokarin da ta ke yi na ganin bankunan kasuwanci sun bi umarnin Babban ba5nkin Najeriya (CBN), ya bayar kan raba sabbin takardun kudi da aka sauya fasali.

Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta kara da cewa binciken ya biyo bayan daya daga cikin ayyukan hukumar na tabbatar da cewa bankunan kasuwanci ba su karya dokar CBN ba.

“Lokacin da tawagar sa ido ta ICPC ta ziyarci bankin ta gano wasu makudan kudade a cikin asusun bankin, an sanar da su hakan ya saba wa dokar CBN.

“Mun gano miliyan biyar kadai suka rabawa rassansu,” in ji ICPC.

Hukumar ta tabbatar da cewa an kama manajonin bankunan, amma daga bisani aka ba da belinsu bayan gudanar da bincike.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta kama manajan bankin Keystone da ke Mararaba a Jihar Nasarawa saboda ya bata wa kwastomominta rai wajen hana su sabbin takardun kudi.

“Tawagar ICPC, a yayin da take gudanar da ayyukanta na yau da kullum, ta gano cewar injinan ATM na bankin ba sa bayar da sabbin kudin lamarin da ya saba da dokar sa aka bayar.

“Sai bayan da aka kama shi kuma aka samu karin haske daga CBN, cewar ATM din bankin ya fara bayar da dubu biyar ga wadanda ba kwastomomin bankin dubu goma ga kwastomomin bankin,” in ji ICPC.