✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan na zama Shugaban Kasa yajin aikin ASUU zai zama tarihi – Kwankwaso

Ya ce in aka bibiyo tarihin mulkinsa a Kano, ba ya wasa da ilimi

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce daga ranar da ya zama Shugaban Kasa an daina yajin aikin malaman jami’o’i a Najeriya.

Kwankwaso wanda har ila yau tsohon Ministan Tsaro ne kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano ya bayyana hakan ne a wata hirar ta musamman da manema labarai a Gombe, inda ya ce da zarar an zabe shi malaman jami’a za su daina kuka.

Yace in ban da harkar siyasa da ya shiga da yanzu shi Farfesa ne, inda ya ce malaman jami’a ’yan uwansa ne zai zauna da su ya saurare su.

“A siyasar ma ni ba irin wanda za a tambaya ina satifiket dinsa bane ya tsaya kame-kame ko ya ce ya bata ba ne,” inji Kwankwaso.

Ya kuma ce bangaren da zai bai wa fifiko shi ne na ilimi kamar duk wanda ya san Kano lokacin yana Gwamna ya san ya bar tarihi a Jihar wajen inganta fannin.

A cewarsa, ba zai kwashe kudin Najeriya don biya musu bukata ba, zai duba matsalar ce tun daga farko ya dakile ta, yana mai cewa ba zai kwashe kudin kasa ba, kuma ba zai bari a kwashe ba dole sai da dalilin abin da za a yi da kudin.

Yace idan ya zama Shugaban kasa, duk wani azzalumi zai kama shi ya kai gidan gyaran hali idan ya gyara halin sannan a fito da shi.

Daga nan sai dan takarar ya yi kira ga malaman jamio’in da su yi wa Allah da Manzonsa su koma Aji domin gwamnati ba kallon su za ta yi ba.