Idan za a yi gaskiya a zaben kananan hukumomin Kano PDP za ta sami nasara – Doguwa | Aminiya

Idan za a yi gaskiya a zaben kananan hukumomin Kano PDP za ta sami nasara – Doguwa

dan takarar shugaban karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano, a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Haruna Ali Rabi’u Doguwa ya ce idan har za a bayar da kayan aiki a yi zabe na gaskiya a zaben kananan hukumomin da za a gudanar a ranar 17 ga Mayu, Jam’iyyar PDP za ta sami nasara.
Alhaji Haruna Ali Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce ganin yadda Jam’iyyar PDP take cin Jam’iyyar APC kamar wutar daji  a halin yanzu a jihar akwai alamun nasara gare ta a zaben da za a gudanar matukar za a yi zabe na gaskiya.
Ya ce tun daga lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya koma PDP, jam’iyyar ta samu martaba da daukaka a jihar a kullum jam’iyyar tana kara samun magoya baya a jihar.
Alhaji Haruna Doguwa ya ce ya fito takarar ce domin ya yi abubuwan da za su kawo ci gaba a karamar Hukumar Doguwa.
Game da matsalar tsaro da ake fama shi a kasar nan kuwa, ya ce ya kamata kowa ya sani cewa yana da gudunmawar da zai iya bayarwa kan zaman lafiya da ci gaban kasar nan.