✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iker Casillas ya koma Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta sanar da cewa tsohon mai tsaron ragarta, Iker Casillas, ya koma kungiyar a matsayin mataimakin darekta a wata…

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta sanar da cewa tsohon mai tsaron ragarta, Iker Casillas, ya koma kungiyar a matsayin mataimakin darekta a wata gidauniyarta mai suna Real Madrid Foundation.

A sanawar da kungiyar ta fitar a shafukanta na dandalan sada zumunta, ta bayyana tsohon tauraron nata a matsayin jakadanta kuma mafi kyawun mai tsaron raga a tarihinta.

Iker Casillas ya lashe kofuna 19 a tsawon shekaru 25 da ya shafe a matsayinsa na dan wasa a kungiyar.

Daga cikin kofunan da Iker Casillas ya lashe a kungiyar da ya wakilta a tsawon shekaru 25 sun hadar da; Kofunan Zakarun Turai guda 3, Kofin Zakarun Duniya 3, Kofunan Zakarun Turai na Super Cup 2, Kofunan La Liga 5, Copa del Rey 2, da Kofuna 4 na gasar Kungiyoyin Spain wato Spanish Super Cup.

A yanzu tsohon dan wasan zai yi aiki tare da gidauniyar kungiyar mai tallafa wa matasa, da kuma ba su duk wani horo da ya dace a fannin tamola.

Real Madrid ta na alfahari tare da maraba da dawowar tsohon dan wasan nata da cewa tana fatan zai ci gaba da kawo ta amfani da kwarewarsa wajen kawo ci gaba a kungiyar.