✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ilimi Kanawa su ke bukata ba gadar sama ba —Kwankwaso

"Kanawa sun fi bukatar ingantaccen ilimi fiye da gadojin sama", in ji Kwankwaso.

Tsohon Gwamnan jihar Kano,  Rabiu Musa Kwankwaso ya soki lamirin Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje kan ciyo bashi domin gina sabuwar gadar sama a unuguwar Hotoro da ke Kano.

Kwankwaso ya ce ciyo bashin kudi N20b don gina gadar, wanda y ace aikin ba hurumin gwamnatin jiha bane na gwamnatin tarayya ne.

Tsohon Gwamnan wanda ke wadannan kalaman yayin wata tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC a ranar Juma’a ya ce jama’ar Kano sun fi bukatar ilimi sama da gadar sama a yanzu.

Idan ba a manta ba, a cikin makon nan ne Gwamna Ganduje ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da gabatar masa da zanen gadar da zai gina a unguwar Hotoro dake cikin birnin Kano, wadda za a sa mata sunan Shugaban Kasa da zarar an kammala.

“Duk da cewar gina gadar sama na da matukar amfani, amma a yanzu Kano ta fi bukatar a mayar da hankali wajen ba wa ’ya’yanmu ilimi mai inganci tare da sama musu abubuwan dogaro da kai,” inji shi.

Ya kara da cewa ba tunani ne mai kyau ba, a ce an ciyo bashin da ba za a iya biya ba don gina gadar sama da shi, wanda daga karshe gwamnati mai zuwa za a gadar wa da bashin.

Kwankwaso, ya ce bayan barinsa mulki bai bar wa jihar bashin ko sisi ba, amma abun mamaki shi ne yanzu ana bin jihar bashin N185b.

Kazalika, ya kara da cewa duk ayyukan gadar sama da gwamnatinsa ta yi jihar, ta yi su ne da kudaden shigar da ta tara ba tare da ciyo bashi ba.

Za mu rushe wuraren da Ganduje ya sayar a 2023

Da yake Magana kan filaye da wuaren da gwamnatin jihar ta sayar, tsohon Ministan Tsaron Najeriya ya sha alwashin cewa idan suka karbi mulki a 2023 za su rushe dukkan wuraren.

Da aka masa tambaya cewar gwamnatinsa ta ba mutane kyautar filaye, Kwankwaso, ya ce “Ban taba rike mukamin Kwamishinan Kasa ba a lokacin mulki na ba, kuma babu wani waje da za a ce gashi an bayar da shi dauke da sa hannuna ba.. A lokacin, ba mu sayar da filayen gwamnati ba, ko kuma filayen masallatai, ma’aikatu ko kuma asibiti ba, idan kuma har akwai aje a rushe su.

“Dukkan wani waje da yake mallakar gwamnati ne, wannan gwamnati ta sayar, dole ne a dawo da su ko kuma a rushe su komai daren dadewa. Ko da kuwa ginin ya kai hawa 1,000 dole a dawo da wurin yadda yake,” inji Kwankwaso.