✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Illolin makaman Nukiliya

Saboda illar makaman Nukiliya, ana kiransu da makaman karedangi.

Su dai makaman Nukiliya wato makaman karedangi, ana kiransu haka ne saboda irin barnar da suke yi, su al’umma da dama suke illatawa ba mutum daya ko biyu ba.

A makon jiya ne fada ya barke a tsakanin kasashen da ake ganin suna da wadannan makamai.

Kasashen da ake ganin sun mallaki makaman Nukiliya su ne Amurka da Rasha da Ukraine.

Akwai ma Birtaniya, China da Koriya ta Arewa, sai Faransa da Isra’ila. Akwai kuma Indiya da Pakistan, sai kasar Iran. Sauran kananan su ne Masar da Afirka ta Kudu.

Ukraine da ake gani kamar karamar kasa bincike ya nuna tana da makaman kare dangi fiye da 3,000.

Ana tsoron barkewar yaki a tsakanin kasashe masu makaman Nukiliya saboda kada su harba su.

Ba kamar sauran makaman yaki irin su bindiga mai harshashi da nakiyoyi da bama-bamai ba, su wadannan makamai ko ba a saita mutum da su ba, idan aka harba su a sararin sama to duk wanda yake yankin da abin ya faru yana iya mutuwa kosamun illa a lafiyarsa.

A wani faifan bidiyo da na gani a kwanakin baya, wanda a ciki aka yi hira da tsofaffin sojojin Ingila da suka yi aikin gwajin wadannan makamai a tsibirai daban-daban (domin a tsibirin da ba kowa ake gwada su), dukkansu sun yi amanna dan Adam bai taba kera wani abu mai hadari fiye da makamin Nukiliya ba.

Suka ce a lokacin idan sun je harba makaman, duk da cewa suna nesa da wurin da aka harba, nisan da aka yarda babu illa idan aka tsaya, akan ce musu da sun harba su juya baya, su sa hannayensu su rufe fuskokinsu na tsawon mintuna.

Amma suka ce ko sun rufe ido hasken da ke tashi a wurin yakan sa duk da idanunsu a rufe ne suna ganin kashin hannayen da suka rufe idanun nasu da su.

Zafin turirin da sukan ji kuwa, suka ce suna ji kamar wani mutum ne da wuta ta kama ya zo ya ratsa ta jikinsu ya wuce.

Suka kara da cewa duk abokan aikinsu da suka riga mu gidan gaskiya bayan sun yi ritaya, cututtukan daji ne yawanci ke ajalinsu saboda wannan aiki da suka yi a baya.

Babu babban misalin makami mai guba da aka taba amfani da shi a wurin yaki wanda ya girgiza ita kanta wadda ta harba kamar makamin da Amurka ta harba a garuruwa biyu na kasar Japan a 1945 wato garuruwan Hiroshima da Nagasaki.

Makaman a tsakiyar gari kawai aka jefa su a filin Allah, amma kan gari ya waye an ce mutane fiye da dubu dari ne suka mutu a garuruwan biyu, wadansu dubu darin kuma cikin makonni da yin abin.

Wannan ta faru ne saboda karfin girgizar garin da bam din ya sa da karfin wani turirin maganadisu mai kona jiki tun daga fata har cikin bargo da ake kira gamma radiation wanda idan bai kashe mutum a lokaci guda ba, zai iya janyo rikidewar kwayoyin halitta na jiki ko su jawo ciwon daji.

Allah Ya ci gaba da kare mu daga irin wadannan bala’o’i, amin