✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Imam Malik: Makarantar kyawawan dabi’u (2)

Daga Hudubar Sheikh Abdulbari Assubaitiy Masallacin Annabi (SAW), Madina   Domin haka mutane masu bayar da sadaka da wadanda suke tafiyar da rayuwarsu a tafarkin…

Daga Hudubar Sheikh Abdulbari Assubaitiy

Masallacin Annabi (SAW), Madina

 

Domin haka mutane masu bayar da sadaka da wadanda suke tafiyar da rayuwarsu a tafarkin Allah da malamai da masu yada Musulunci da masu yi wa Musulunci hidima ta fannoni da dama duk suna yin aiki na kwarai – idan suka yi da ikhlasi da kyakkyawar niyya.

Duk lokacin da aka tambayi Imam Malik (Rahimahullah), yakan shaida wa mai tambayar cewa: “Ka tafi ka ba ni dama in yi nazari a kanta.” Idan mai tambayar ya tafi, sai almajiran Imam Malik su tambaye shi dalilin abin da ya yi, sai ya amsa da cewa: “Ina tsoron wata rana (ta haduwa da) Mai tambaya (Allah) kuma wannan rana ce (mai firgitarwa).”

Mutanen Yamma (Maghrib) sun aiki wani mutum ya tambayi Imam Malik (Rahimahullah) a kan wasu abubuwa. Mutumin ya yi wa Imam Malik wata tambaya, amma sai ya ce: “Ban sani ba, domin ba mu san wannan abu ba a nan kasarmu, kuma ba mu ji wani daga cikin malamanmu ya ce wani abu a kansa ba, amma za ka iya sake dawowa.”  Washegari mutumin ya koma ga Imam Malik sai Malik ya ce masa: “Ka yi min tambaya amma ban san amsarta ba!” Sai mutumin ya ce: “Ya Abu Abdullah! Na zo ne daga wadansu mutane wadanda suke tunanin babu wani mutum a duniya wanda yake da ilimi kamarka!” Sai Malik ya ce: “Ni ma ban cika goma ba!”

Sannan an taba tambayarsa, sai ya ce wa mai tambayar ya ba shi lokaci zai yi bincike, sai mutumin ya ce: “Amma ai al’amarin mai sauki ne.” Sai Malik ya ce: “Ai babu wani abu mai sauki a fagen ilimi. Ko ba ka ji fadin Allah ba ne cewa: “Lallai ne Mu, za Mu jefa maka magana mai nauyi.” (K:73:5).

Imam Malik (Rahimahullah) ya kasance yana cewa: “Masu ilimi da fahimta da na iske a kasarmu, idan aka tambayi dayansu kan wani batu, yakan ji kamar zai fadi ya mutu. Amma mutanen zamaninmu su kuma suna son su rika bayar da fatawa (ba tare da damuwa ba). Da sun san abin da za su je su iske a gobe (Ranar Hisabi) da ba su yi haka ba. Umar da Ali da Alkama (Allah Ya yarda da su) suna daga cikin mafifitan sahabban Annabi (SAW), amma duk lokacin da wani ya tambayi daya daga cikinsu, sai ya tambayi ’yan uwansa sahabbai kafin ya bayar da amsa a kanta. Amma abin takaici shi ne bayar da fatawa ta zama abin alfahari ga mutanen zamaninmu.”

Wadannan fa fitattu kuma kwararrun masana ne da suka cika duniya da iliminsu da kyawawan ayyukanku, amma duk da haka sukan ce: “Ba mu sani ba!”

Don haka da mamaki ka ga wadansu mutanen da ba su san komai ba game da dokokin addinin Musulunci amma duk da haka suna muzanta su ta hanyar yin magana a kan abin da aka yarda da shi kuma aka halatta. Har ta kai wani batu kan dokar Musulunci kan iya zuwa a lokacin wani taro ba tare da dukkan mahalartarsa – tare da bambancin fagen iliminsu – sun bayar da nasu ra’ayoyin ba, misali suna cewa ‘a fahimtata…’ ko ‘bisa abin da nake da yakini…’ da sauransu.

SubhanAllah! Yaushe al’amarin halattawa da haramtawa ya zamo wani batu na tattaunawar jahilci da ra’ayi?

Idan aka ce injiniya ya zamo likita ya rika ba mutane magunguna, me za ku ce a kansa, kuma mene ne zai kasance makomarsa? To mene ne makomar mutumin da ke caccakar dokokin Musulunci yana yin magana a kan halattawa da haramta abubuwa ba tare da ilimi ba, musamman a muhimman abubuwa da idan Umar (Allah Ya yarda da shi) ne lamarin ya zo masa sai ya tara dukkan sahabban da suka halarci Yakin Badar su taimaka masa wajen warware matsalar?

Amma abin takaici bayar da fatawa a zamaninmu ya zamo wani fage da duk wanda yake son ya yi suna ko yake neman girmamawar mutane zai fito ya bayar da ita koda za ta sa Allah Ya yi fushi da shi!

’Yan uwa a cikin imani! Batutuwan da suka shafi imani a Musulunci abubuwa ne da ba su bukatar wani ya bayar da wani ra’ayi nasa na daban. Kuma haka batutuwan da suke da madogara daga Alkur’ani da Sunnah ko wanda malamai suka yi ittifaki a kai.

Kuma wajibi ne a kan dukkan Musulmi su bar masana su yi magana a kan abin da ya shafi ilimi, kada su shiga batun da ya shafi halal da haram alhali ba su da ilimi a kai.

Imam Malik (Rahimahullah) ya ce: “Duk wanda yake son ya bayar da amsa a kan wata tambaya, to ya bijiro da kansa cewa yana tsaye ne a tsakanin wuta da Aljanna, ya tsaya ya yi tunani kan yadda zai kubuta a Ranar Kiyama kafin ya bayar da amsa.”

Wadansu mutane sun dauka wadancan malamai sun kware ne kawai wajen al’amuran da suka shafi sabani da tattauna batutuwan da suka shafi ilimi, ko kuma zamaninsu sun rika sukar Hadisan da suke gyara zukata su tunatar kan Aljanna da wuta.

Domin a san cewa zamaninsu ya hada fagagen ilimi daban-daban, bari mu ji abin da Imam Malik ya ce ga wani dan uwansa da yake sukarsa: “Ka tunatar da kanka kan zafin mutuwa da abin da za ka hadu da shi da abin da zai zamo makomarka bayan ka mutu; da tsayuwarka a gaban Allah da hisabin da za a yi maka da kuma makomarka ta karshe Aljanna ko wuta. Ka yi shiri ga wannan lokaci kan yadda za ka samar da sauki ga kanka a lokacin, domin lokacin za ka ga abin da zai samu wadanda suka ja wa kansu fushin Allah da figircin irin bala’in da suke ciki, za ka ji kukansu a cikin wuta da bakaken fuskokinsu, ba su iya gani ko magana, za su rika kururuwar hallaka, kuma abu mafi girma daga haka, Allah zai kawar da kanSa daga gare su, za su yi ta neman Ya ba su amsa kan kukansu amma sai Ya ce: “Ku tafi (da wulakanci)  a cikinta, kada ku yi Mini magana.” (K:23:108). Idan ka san wadannan duka, babu wani abu a wannan duniya da zai kasance babba gare ka da ba za ka sadaukar da shi domin neman ceto a Lahira ba.”

Allahu Akbar! Imam Malik ya yi jinya na kwana 22 kuma ya rasu yana da shekara 87.

Fitaccen almajirinsa, Nafi’u ya ce: Malik ya rasu yana da shekara 87, kuma ya rayu a Madina yana matsayi Muftinta na shekara 60.”

Ya Allah! Ka yi rahama ga Imamu Malik wanda ya ce: “Na iske wadansu mutane a Madina wadanda ba su da wasu laifuffuka amma suna maganganu a kan laifuffukan wadansu mutane, don haka sai mutane suka kirkiro musu laifuffuka. Kuma na iske wani rukuni na mutane a Madina da suke da laifuffuka amma suka guje wa yin magana kan laifuffukan sauran mutane, sai mutanen su ma suka kame daga yin magana a kan laifuffukansu.