✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IMF ya shawarci CBN ya kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudi

IMF ya bukaci kara wa'adin duba da yadda harkokin kasuwanci suka tabarbare.

Asusun Ba Da Lamuni na Duniya (IMF), ya bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya duba yiwuwar kara wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudi daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Asusun a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ya ba da misalin yadda aka samu tabarbarewar kasuwanci da kuma tattalin arziki sakamakon canjin kudi.

“Bisa la’akari da wahalhalun da canjin kudi ya kawo da kuma cikas ga kasuwanci da kuma biyan kudade sakamakon karancin sabbin takardun kudi da jama’a ke fuskanta, duk da matakan da CBN ya bullo da shi na magance kalubalen da ake fuskanta game da canjin takardun kudi, IMF na bukatar CBN ya duba yiwuwar kara wa’adin daga ranar 10 ga watan Fabrairu,” in ji IMF.

Sanarwar ta fito ne daga hannun Laraba S. Bonnet, Manajar Ofishin Wakilin Mazauna Najeriya a madadinsa.

Bayanin na zuwa ne bayan da kotun koli ta hana CBN kin kara wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kotun ta bayar da umarnin ne a wani hukunci da ta yanke kan karar da gwamnatocin Jihohi uku suka shigar a gabanta.

Tun da farko dai CBN ya kayyade wa’adin zuwa ranar 31 ga watan Janairu amma ya kara wa’adin sakamakon matsin lamba daga ‘yan Najeriya.