✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

In aka raba Najeriya ba bangaren da zai zauna lafiya – Niyi Akintola

Aminiya ta samu tattaunawa da Cif Niyi Akintola wanda Babban Lauya ne a Najeriya (SAN) kuma dan siyasa da ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar…

Aminiya ta samu tattaunawa da Cif Niyi Akintola wanda Babban Lauya ne a Najeriya (SAN) kuma dan siyasa da ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Oyo a Jam’iyyar APC a zaben 2019. Tattaunawar ta tabo batun ’yancin kai da sake fasalin kasa inda ya ce, ya in aka raba Najeriya ba bangaren da zai zauna lafiya, za a tsunduma ne cikin yaki. Ya ce kamata ya yi a koma baya kan bayanin da marigayi Sardaunan Sakkwato Alhaji Ahmadu Bello ya yi a 1953 cewa sai mun gano matsalolinmu muka girmama juna ne za mu kai ga nasara.

Kana ganin Najeriya ta ci gaba a shekara 60 da samun ’yancin kai?

Har yanzu ba mu ci gaba ba, domin babu kishin kasa a zukatanmu kuma ga matsaloli da yawa da suka hana mu ci gaba, kamar matsalar tsaro da nuna bambancin addini da kabilanci da siyasa da cin hanci da rashawa da matsalar sojoji wadanda su ne suka haifar da gurguncewar tafiyar.

Da sojoji sun kyale mu ba su yi juyin mulki a 1966 ba to da mun kai ga nasara. Wasu kasashe kamar Malesiya da Koriya ta Kudu da Indiya da muka samu ’yanci kusan a tare sun ci gaba sosai.

Wacce hanya ya kamata Najeriya ta bi don samun ci gaba?

Ya kamata mu zauna bisa teburi daya mu tattauna da juna domin gano dalilin da ya hana mu ci gaba. Ya kamata mu koma baya ga wurin da iyayenmu su Sardaunan Sakkwato da Cif Obafemi Awolowo da Cif Nnamdi Azikwe suka ajiye mu. Akwai taron da wadannan iyayen kasa suka yi a 1953 inda a tattaunawarsu Cif Azikwe ya kawo shawarar cewa mu manta da bambace-bamcenmu amma nan take Sardauna Ahmadu Bello ya nuna rashin amincewarsa inda ya ce sai idan mun girmama irin wadannan bambance-bambance da girmama juna ne za mu kai ga nasara.

Saboda haka nake ganin idan har muka yi aiki da matsayin Sardauna a kan abin da ya fadi a wancan lokaci to Najeriya za ta zauna lafiya da hakan ya kawo mana ci gaba.

A daidai wannan lokaci wasu kungiyoyi suna fafutikar ganin an kafa kasar Ooduwa a nan Kudu maso Yamma da kasar Biyafara a Kudu maso Gabas kana ganin wannan abu ne mai yiwuwa?

Wallahi tallahi ba zai yiwu ba, domin rabuwar Najeriya babbar matsala ce ga dukkan bangarorin kasar nan. Zan iya tunawa mutanen Arewa ne suka fara neman a raba Najeriya a 1957 a yayin da mutanen Kudu maso Gabas suka nemi a raba qasar a 1966, mu kuma mutanenmu a Kudu maso Yamma muka biyo baya ta neman irin wannan bukata.

Idan har aka raba Najeriya zuwa kasashe, to mun jawo wa kanmu wahalar da ba za mu iya maganinta ba. Misali, idan an kafa kasar Yarbawa ta Ooduwa to mummunar gaba za ta kara fitowa fili a tsakanin al’ummomin garuruwan wannan sashi.

Da ma akwai ta a kasa inda a yanzu haka yankin Ijebu da Egba a Jihar Ogun da yankin Legas suka mamaye dukkan manyan mukaman kasar
nan da ake ware wa Yarbawa.

Misali, tsofaffin shugabannin Najeriya Olusegun Obasanjo da Ernest Shonekan da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo dukansu ’yan Jihar Ogun ne. Kuma yanzu haka idan an bayar da manyan mukaman kasa 10 ga Yarbawa to ’yan Ijebu da Egba a Jihar Ogun da Legas ne za su kwashe tara daga ciki.

Ka ga kenan idan har aka kafa kasar Ooduwa za mu yi ta kashe juna ne a dalilin danne hakkin da wani sashi ke yi. Idan ka lura sosai za ka gane cewa abin da ke faruwa yanzu haka a kan siyasa a wannan sashi shi ne irin yadda Jam’iyyar PDP ta yi nasara a zaben Shugaban Kasa da ya gabata a jihohin Oyo da Osun da Kwara, Jihar Ondo kuwa ta samu kashi 49.

Hakan ya nuna a fili cewa yunkuri ne na dakatar da jihohin Ogun da Legas daga danniyar da suke yi. Haka lamarin yake a Middle Belt da suka kunshi kabilun Jarawa da Birom da Tibi da Nufawa da Idoma da Ibira da sauransu, wadanda yanzu haka suke yunkurin ballewa daga Arewa.

A ina za a ajiye su idan sun balle daga Arewa. To su ma fada ne zai kaure a tsakaninsu da zai haifar da kashe-kashen juna. A can Kudu maso Gabas ma irin abin da zai faru ke nan idan har aka amince da rabuwar Najeriya zuwa kasashe.

To ina mafita?

Mu zauna a matsayin kasa daya shi ne mafita amma mu yi zaman tattaunawa tsakani da Allah kuma mu koma ga aiki da bayanin da
marigayi Sardauna Ahmadu Bello ya yi shekara 67 da suka gabata cewa mu girmama juna.

Ya kamata kowane sashi ya ci gashin kansa. Idan wannan sashi ya ce zai mayar da hankali a kan ilimi wancan sashi kuma ya ce zai kashe kudinsa
a kan shari’a ko aikin gona ne to sai a kyale kowa ya yi abin da yake so
a cikin kasa daya Najeriya ba tare da danne hakkin wani bangare ba.

Ka san har yanzu Najeriya ba dunkulalliyar kasa ba ce domin
akwai garuruwa da kauyuka masu yawa da kabilu masu yare daban-
daban da addinai. Saboda haka kyale kowa ya ci gashin kansa shi ne
zai sa mu kai ga nasarar dunkulewa waje daya da ci gabanmu.

A shekarun baya ka tava bayar da shawarar cewa ya kamata Najeriya ta yi koyi da salon mulkin tsohon Shugaban Kasar Ghana, Jerry Rawlings kan kashe mutanen da aka samu da laifin cin hanci da rashawa. Shin kana nan a kan bakarka ko ka canja?

Ina nan a kan bakata domin kashi 70 na dukkan matsalolin da muke ciki a Najeriya cin hanci da rashawa ne ya haifar da su. Har ma na kara da shawarar mu yi koyi da irin yadda kasashen Malesiya da Singafo da China suke yi wajen gurfanar da duk wanda aka samu da irin wannan laifi gaban kotu idan an same shi da laifi shari’a ta yanke masa hukuncin kisa.

A Najeriya ce za ka ga wani ya sace kudin da ba zai taba yin amfani da su a rayuwarsa ba, idan ba ciwon hauka ba yaya za ka saci abin da ba zai amfane ka ba ko da za ka yi shekara dubu daya a raye.

Kana ganin salon yaki da cin hanci da rashawa da Shugaba Buhari ya bullo da shi bai isa ba kenan?

Matakin da Shugaba Buhari yake dauka yana da kyau sosai amma hukuncin kisa ne ya dace da irin wadannan mutane. Kuma ka san cewa Shugaba Buhari ya samu kyakkyawar shaidar gaskiya amma shi kadai ne a cikin barayin da suka hana shi gudanar da aiki.

Ya kamata a ji tausayin Buhari da yi masa addu’ar alheri.