✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

In Za Ka Fadi… Sauya sheka a tsakanin ’yan siyasa

An yi jana’izar siyasar akida, batu kawai ake na makomar kashin kai a kasar nan.

Sauya sheka da ’yan siyasa suke yi daga jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, kusan za mu ce ba a taba ganin irinsa ba, domin ba wai kananan ’yan siyasa ba ne har da gwamnoni, domin a baya-bayan nan, mun ga yadda gwamnonin jihohin Ebonyi, Mista David Umahi da na Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade da kuma Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad Matawalle suka canja shekar, sannan mun ga yadda sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da dama suka sauya sheka.

Kusan ba sabon abu ba ne sauya shekar da ’yan siyasa suke yi, amma dai yadda yanzu a wannan lokaci ake tururuwar komawa jam’iyya mai mulki abin na nuna cewa an yi jana’izar siyasar akida a kasar nan, yanzu batu kawai ake na makomar kashin kai, ba wai kishin al’umma da samar musu da ci gaba da dora matasa a kan turba ta kishin kasa da kishin ci gabanta ba, kowa kawai yana duba ina zai shiga inda za a ci gaba da damawa da shi a sha’anin mulki da siyasar kasar nan.

Abin da ya faru a makon jiya, al’ummar Najeriya da yawa sun cika da mamaki da ta’ajibi, inda wadansu suka nuna sun jima da tunanin hakan za ta faru.

Mutane da yawa sun tattauna kan batun sauya shekar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama a zamanin gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo, kuma tsohon Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zabe na tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, Femi Fani-Kayode wanda muryarsa ta yi kaurin suna wajen sukar ’yan siyasar Arewa da Musulmi baki daya.

Femi Fani-Kayode mutum ne da yake da ake zargi da tsananin nuna bambancin addini da kabilanci.

Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, an sha jiyo shi yana sukar manyan ’yan siyasar Arewa da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, galibi kuma yana fakewa ne da sunan addini ko yankin Kudu ya soki gwamnatin.

Babu wani nau’i na cin mutunci da cin zarafi da bai yi wa al’ummar Arewa ba da sunan adawa da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.

Har Shehu Usmanu Dan Fodiyo sai da ya zaga saboda tsananin kiyayyarsa ga mutanen Arewa da sunan hamayyar siyasa.

Kowa ya ga yadda ya nuna goyon bayansa ga shugabannin ’yan awaren Najeriya wato jagoran kungiyar ta’adda ta IPOB, Mista Nnamdi Kanu da kuma tsageran nan na Yamma da ke kokarin kafa kasar Yarabawa zalla wato Sunday Igboho.

Wadannan mutane da suka ci amanar kasa karara Femi Fani-Kayode ya nuna goyon bayansa gare su tare da nuna yana tare da su yana kuma kira a mara musu baya domin abin da suke yi yana yi masa dadi.

Baya ga wannan, Femi Fani-Kayode ya kirkiro wani zagaye na babu gaira, babu dalili da sunan kewaya jihohin da gwamnonin PDP suke mulki domin wai ya ga irin ayyukan raya kasa da suke yi, inda wani dan jarida ya taba tambayar sa wa yake daukar dawainiyarsa a wannan tafiye-tafiye da yake yi, tambayar da ta sosa wa Fani-Kayode rai sosai, domin ji ya yi kamar an ce masa yana yawon maula ne wajen gwamnonin.

Daga bisani ne kuma aka ga ya kulla wata alaka da Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello inda aka gan shi a birnin Lakwaja ya je wajen Gwamnan.

Daga nan ya sake mike kafa har zuwa wajen Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad Matawalle, daga bisani kuma aka ji har an ba shi sarautar gargajiya ta Sadaukin Shinkafi, a jihar.

Tun a wancan lokacin masu fashin baki suka bayyana take-taken Femi Fani-Kayode na shirin sauya sheka ne zuwa Jam’iyyar APC mai mulki, domin yana ganin ba zai iya ci gaba da jure yin azumin siyasa a cikin jam’iyyar adawa ba.

Tun kafin abin da ya faru a makon jiya, an gan shi a gidan Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC ta Kasa, Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni.

A nan ma ta sake tabbata cewa Femi Fani-Kayode ya gama shiri tsaf na tsallakawa jam’iyyar APC, wadda ya zaga ya ci mutunci ya kira ta da jam’iyyar almajirai, ya kira ’yan Arewa da ’yan ta’adda, duk wani nau’i na cin zarafi da cin mutunci babu wanda Femi Fani-Kayode bai yi wa APC da mutanen Arewa ba.

Kwatsam, bayan da ya sauya sheka sai muka ga an yi masa kyakkyawar tarba, an kai shi fadar Shugaban Kasa ya sanya masa albarka, daga bisani kuma aka gan shi a gidan Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami wanda Femi din ya taba kira da dan ta’adda, sai ga shi a gidansa sun ci abinci sun yi raha da juna.

Wannan batu shi ne kusan abin da ya mamaye kafafen sada zumunta kuma ake ci gaba da tattaunawa a kansa har yanzu; Wadansu na yabo, wadansu na kushewa da kiran ana wasa da hankalin jama’a da sunan siyasa ko neman mulki.

Wannan sauya sheka ba komai take nunawa ba illa yunkurin da manyan ’yan siyasa suke yi na tabbata a kan mulki, idan jam’iyyar PDP ta kafa gwamnati su taru a ci gwamnatin da su, idan APC ta kafa su sake taruwa a can a ci da su.

Wannan duk bayan an yamutsa hazo an zagi juna an fadi bakaken maganganu, babu batun siyasar akida da kokarin ceto jama’a daga cikin mawuyacin hali, ko yin adawa ta gaskiya ta ciyar da kasa gaba da kokarin kawo wa al’ummar Najeriya abubuwan ci gaba, burinsu kawai shi ne yaya za a yi su samu su da iyalansu!

Tsarin da ake kokarin dora kasar nan a kai na jam’iyya daya, abin tsoro ne ainun.

Domin ko kasar Amurka da muke koyi da ita, ba tsarin jam’iyya daya take bi ba.

Wannan tsarin ya yi kama da kama-karya wanda a Afirka kawai za ka ga ana yin sa, kuma ga shi ana kokarin yi a Najeriya, kamar yadda muke gani a Uganda da Kamaru da Gabon da Kwango da sauran kasashen Afirka da suke yin tsarin kama-karya da sunan dimokuradiyya.

Wannan kuma, ya sanya dole al’ummar kasar nan su tashi tsaye su bude idonsu, su zabi nagartattun mutane, kada mu yarda da tsarin jam’iyya daya ko biyu, mutane su tashi su wayar da kan al’umma a zabi nagartattun mutane a duk jam’iyyar da suka tsaya a zabe, kamar dai yadda muka ga an yi a Jihar Bauchi a zaben 2019, inda aka zabi wasu jam’iyyun da ba PDP ba kuma ba APC ba, wannan kuma ba yana nufin kada a zabi nagartacce idan ya tsaya takara a APC ko PDP ba ne, duk inda mai nagarta yake a zabe shi ko a ina yake.

Idan jam’iyyun PDP da APC za su dinga sanya wa mutane nagartattun ’yan takara wadanda za su iya share wa al’umma hawaye babu laifi a zabe su, amma kuma al’umma ta waye ta fadaka cewa siyasar dimokuradiyya zabi ne aka ba mutane su zabi wadanda suke so su shugabance su ko su wakilce su, kada kawai mutane su mai da jam’iyyu biyu kadai su ne za a zaba.

Idan mutum ya ga bai samu nasara a APC ba sai ya koma PDP, ko in bai yi nasara a PDP ba, sai ya koma APC, su kuma talakawa an bar su da zagin juna da cin mutuncin juna da sunan hamayya.

Yanzu duk irin zarge-zargen da aka dinga yi wa PDP cewa ita ce ta rusa kasar nan, ta lalata komai, idan aka wayi gari duk mutanen PDP sun tsallaka zuwa jam’iyyar APC shi ke nan su ruwa ta sha, sai a hadu da su a dinga sukar PDP ana cewa ita ce ta rusa kasa ta lalata tattalin arziki?

Talaka ko mai zabe ya zama ba mutunci ana wasa da tunaninsa da hankalinsa, mu yi abin da muka ga dama a PDP ranar da duk muka koma APC shi ke nan mun zama mutanen kirki?

Anya za mu ci gaba a haka kuwa?

Yasir Ramadan Gwale ([email protected]) 08023917104 (Tes kawai)