✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina aka kwana kan aikin yashe teku zuwa Arewa?

Aminiya ta gano har yanzu kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu

Duk da kashe biliyoyin Naira da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen kula da kuma yashe teku zuwa Arewa, musamman Kogin Kwara, don bai wa jiragen ruwa zarafin yin jigila a kowane lokaci da bunkasa harkokin tattalin arziki, har zuwa yanzu haka ba ta cim ma ruwa ba, kamar yadda Aminiya ta gano:

Za a iya cewa Kogin Kwara da aka fi sani da Kogin Neja a Ingilishi daya ne daga cikin manyan albarkatun da Allah Ya huwace wa kasar nan da idan aka alkinta shi yadda ya dace zai iya zama hanyar da kasar nan za ta dogara da ita ta fuskar fadada hanyoyin samun kudin shiga gare ta.

Kogin Kwara da rassansa sun kasance muhimman hanyoyi sufuri gabanin mulkin mallaka da lokacin Turawan mallakar har ma da bayan mulkinsu.

Batun aikin yashe kogin don ya hade da teku ya ci gaba da zama wani aiki da tun bayan samun ’yancin kai gwamnatoci suka yi ta hankoron yi amma sai da marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ya zama Shugaban kasa aka sa dan ba na aikin a zahiri.

A ranar 1 ga Disamban 2008, marigayi Shugaba ’Yar’aduwa ya samu nasarar karya kwarin aikin da ya dade ana yunkurin yi tun daga lokacin mulkin mallaka inda ya rattaba hannu a kan kwantaragin yashe kogin daga Warri zuwa Baro a Jihar Neja a kan Naira biliyan 34.8.

A yunkurin tabbatar da aikin ya wanzu, marigayin ya kaddamar da aikin a ranar 10 ga Satumban 2009 a Lakwaja, babban birnin Jihar Kogi; tare da tsarin kammala shi a cikin shekara uku.

An kuma sake nazartar kwangilar inda a ranar 2 ga Nuwamban 2011 Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince da kara kudin aikin da Naira biliyan 8.5, inda kudin kwangilar ya koma Naira biliyan 43.3. karin an yi shi ne bisa la’akari da hauhawar farashin kayayyaki da ake samu.

Wani injiniya kan harkokin koguna da teku da ke Lakwaja, Injiniya Mathias Oke, ya ce yunkurin da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi na ganin an yashe kogin da kudin Asusun Rarar Man Fetur (PTF) ya samu cikas.

Ya ce daga cikin dalilan yashe kogin shi ne a mayar da shi yadda jirage za su rika jigilar kayayyaki daga teku zuwa Arewa don zaburar da harkokin tattalin arziki da rage nauyi da hadurran a kan hanyoyin mota tare da samar da guraben ayyuka ga ’yan Najeriya.

Hukumar Kula da Sufurin Ruwa ta kasa (NIWA), wadda ke da alhakin sa-ido a kan safara a cikin kogunan Najeriya, ta ce fiye da jihohi 20 ne a Najeriya suke da alaka da sufurin ruwa a tsakaninsu ta kogunan da suka hade su.

A cewar Hukumar NIWA, hanyoyin sufurin ruwa a Najeriyar sun hada da 12 a manyan koguna da rafuka da gulabe da tafkuna da wasu ruwan da suka hade iyakokin jihohin; wadanda jimillarsu ta tasam ma fiye da kilomita dubu 10.

Sanata Binta Masi Garba, wadda ita ce Shugabar Hukumar Daraktocin Hukumar NIWA, ta ce daga cikin fiye da kilomita dubu 10 na hanyoyin sufurin ruwa a Najeriya, kashi 30 ne kacal wato kimanin kilomita 3,800 jirage suke iya sufuri a cikinsu.

“Hakkin mayar da kilomita dubu 10 wurin da jirage za su iya jigila a kowane lokaci ya rataya ne a wuyar Hukumar NIWA, don samar da wata hanyar sufurin jama’a da kayayyaki ga ’yan Najeriya maimakon hanyoyin mota da layukan dogo,” inji ta.

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dora daga inda wanda ya gada ya tsaya, wanda hakan ya sa aka ci gaba da gudanar aikin cikin nasara. A shekarar 2011, rahotanni sun ce Shugaba Goodluck ya fitar da kudi domin fara aikin yashe kogin daga Warri zuwa Baro.

A Agustan 2014, tsohon Shugaban ya ce gwamnatinsa ta kammala aikin yashe Kogin Kwara daga Warri zuwa Baro mai nisan kilomita 527 a yayin wani Taron Baje Koli na farko da Hukumar NIWA ta shirya a Legas.

Shugaba Jonathan wanda Ministan Sufuri Alhaji Idris Umar ya wakilta, ya yi kira ga masu zuba jari su yi amfani da yashe kogin da aka yi wajen karfafa harkokin cinikayyarsu.

Ita ma Hukumar NIWA ta yi bikin kan aikin jim kadan bayan kammala aikin yasar a watan Agustan 2011 lokacin da Kamfanin Sufurin Ruwa na NINON, ya yi jigilar tan 300 na tayil wanda yake daidai da tireloli 20 daga Lakwaja ta cikin kogin da aka yashe zuwa garin Anaca a Jihar Anambra.

Haka ma tsohon Ministan Sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya fada wa manema labarai cewa an kammala aikin yashe kogin.

Ya fadi haka ne yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Kula da Sufurin Teku na Majalisar Dattijai domin kare kudirin kasafin kudin ma’aikatar.

Koda yake, shekaru da dama bayan shagali da ayyanawa a hukumance cewa an kammala aikin yashe Kogin Kwara, bisa ga dukkan alamu har yanzu ba ta canza zani ba, saboda babu wata shaida ta ganin jiragen dakon kaya suna jigila ko yada zango ko saukewa da daukar kaya a kogin.

Kuma a bayyane take masu zuba jari na dari-darin amfani da kogin wajen hada-hada. Aminiya ta gano cewa jan kafa wajen gudanar da hadahadar kasuwanci duk da ikirarin kammala aikin yashe kogin yana diga ayar tambaya ga masu ruwada-tsaki a fannin.

Mista Akpan Edem, wani injiniya da ya yi ikirarin yana hada-hadar albarkatun da ke cikin ruwa a Lakwaja, ya ce tafiyar hawainiya wajen gudanar da hada-hadar cinikayya a kogin bayan ikirarin yashe kogin, tana neman gaskata batun da Kwamared Aminu Umar, Shugaban kungiyar ’Yan Najeriya Mamallaka Jiragen Ruwa (NISA) ya yi a 2016 cewa akwai alamomin tambaya dangane da aikin yashe kogin.

An ruwaito shi yana cewa, “Muna ta jin cewa wai an yashe Kogin Kwara har zuwa Warri, amma abin tambaya a nan shin hakan ya sa jiragen ruwan da suke jigila sun karu a wadannan koguna? kungiyar NISA ta yi amanna cewa sam babu batun wani aikin yashe kogi da ya gudana,” in ji shi.

Mista Benjamin Okolo, wanda yake wakiltar mazabar Dekina/Bassa a Majalisar Wakilai a Jam’iyyar APC, shi ma an ruwaito shi ya dago muhawara a zauren majalisar.

Ya ce duk da cewa an ba da kwangilar yashe kilomita 118 daga Anaca zuwa Idah, ga kamfanonin ban Oord Nigeria Limited a kan Naira biliyan 10.4, da kuma kilomita 108 daga Idah zuwa Jamata, a kan Naira biliyan 13.8; har yanzu lamarin yana nan jiya-i-yau. B

abu wani karin haske kan ko kwamitin da aka ce Majalisar Wakilai ta lokacin ta kafa don bincikar aikin ya mika rahotonsa kafin wa’adin majalisar ya kare.

Har wa yau, Aminiya ta gano cewa shekaru bayan ikirarin kammala aikin yasar kogin akwai batutuwa masu cin karo da juna da suka dabaibaye aikin.

Alal misali, Kwamared Idris Maliki, Babban Daraktan kungiyar Kare Hakkin dan Adam da Sasanta Rigingimu (CHRCR), ya ce akwai siyasa a batun aikin yashe kogin.

“Lamarin ya shallake tunanina wai a ce bayan wadannan shekaru da ikirarin aikin yashe Kogin Kwara amma har yanzu babu wani muhimmin abu da ke gudana a kogin. Ya kamata su fayyace mana ko dai aikin shi ma ya bi shanun Sarki ne ko kuma a’a,” inji shi.

Ya kara da cewa gaba daya aikin ya zama abin al’ajabi Sai dai a cewar, Babban Manajan Sashen Hulda da Jama’a na Hukumar NIWA, Jibril Darda’u, hukumar ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na yashe kogin a tsakanin shekarun 2009 zuwa 2011, yana mai cewa shekara biyu bayan nan, an gudanar da aikin kula da yasar da aka yi wa kogin ta hanyar aiki da kwararrun ma’aikata da na’urorin hukumar domin rage kudin da za a kashe a aikin.

Ya ce gudanar da aikin yasar ya sa hanyar ruwa daga Warri zuwa Baro ta zama inda jiragen ruwan suke jigila don gudanar da halattattun hada-hada yana mai nanata cewa an mayar da kogin bigiren da masu zuba jari za su tafiyar da harkokinsu.

“An kammala duk aikin yasa da kuma na kula da inda aka yashe, ana ta hada-hadar jigilar ruwa a kogunan sannan Hukumar NIWA ta dukufa wajen zawarcin masu zuba jari,” inji shi.

Ya kara da cewa an rarraba aikin zuwa gida biyar inda aka bai wa kamfanonin Fung Tai Eng Company Nigeria Limited da International Serbice Nigeria Limited da ban Oord Nigeria Limited da Williams Lloyds Technology Company Limited.

Darda’u, wanda ya ce an kashe Naira biliyan 36 a ainihin aikin yashe kogin, ya ce kogin yana bukatar a kula da inda aka yashe a-kai-a-kai bayan kowace shekara biyu don hana kogin sake tara laka da yashin da za su toshe hanyoyinsa; wadanda idan aka bari sai an sake gudanar da ainihin aikin yasar a nan gaba.

Har wa yau, a taron kwanan nan na mambobin hukumar da aka sake wa fasali da ya gudana a Lakwaja, Sanata Binta Garba Masi ta ce aikin yashe kogin yana da cin kudi, don haka hukumar ba ta dogaro kacokan da gwamnati tana neman tallafi daga kasashen duniya da sauransu wajen hada hannu a aikin.

Babban Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar NIWA, Cif Kingsley Moghalu, ya nuna damuwa kan abin da ya kira rashin samar wa hukumar isassun kudi a kasafi.

Ya ce hakan yana daga cikin dalilan da suke haifar da tsaiko a aikace-aikacen hukumar.

Ya ci gaba da cewa mahukuntan NIWA na duba yadda za su inganta ayyukanta. Masu ruwa-da-tsaki a bangaren harkokin sufurin teku kamar Hukumar Kula da Masu Jiragen Ruwa ta Najeriya da kungiyar Masu Jiragen Ruwa da kera su ta Najeriya ciki har da kungiyar Masu Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (NASSI) da sauransu bakinsu ya zo daya a kan ikirarin na Moghalu kan karancin kudaden a kasafin hukumar, inda suka yi ittifakin cewa lamarin yana haifar da tafiyar hawainiya ga ayyukan hukumar. Masu ruwa-da-tsakin wadanda Okolue A. Ify, Daraktan Shiyyar Arewa ta Tsakiya na Hukumar Masu Jiragen Ruwa ya jagoranta sun yi alkawarin samar da kyakkyawar hanyar aiki tare da Hukumar NIWA don kammala ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu da inganta hadahadar sufurin jiragen ruwa don ci gaban tattalin arziki.

Kwararru sun ce idan aka yashe kogin yadda ya kamata kuma jirage suka kama jigila a ciki, Gwamnatin Tarayya za ta iya samun Naira biliyan 23 a shekara 30 na hayar da ta bayar kafin ta amshe ragamar gudanar da wajen.

Game da batun janyo hankalin masu zuba jari a fannin sufurin ruwa na cikin gida kuwa, Babban Daraktan Hukumar Masu Jiragen Ruwa ta Najeriya, Mista Edwin Ignatius, ya ce yashe kogin ba wai ya tsaya kawai ga yasar yashi domin samar da hanyoyin da jirage za su rika wucewa ba ne, a’a yanayin ruwan da kuma tashohin jiragen su ne abubuwan da masu zuba jari suke la’akari da su.

Ya ce lallai ne kogin da aka yashe a inganta yanayinsa ta yadda zai yi daidai da wasu ka’idoji domin bai wa masu zuba jari da kasashen duniya kwarin gwiwar shiga a dama da su. A cewarsa, Sojin Ruwan Najeriya ne kadai ke da sahalewar duniya na nazartar kogi domin yiwuwar a daga darajarsa.

Ya ce nazarin hakan ya zama dole domin fahimtar yawan laka ko yashi da sauran abubuwan da suke kwance a karkashin kogunan sannan a yi batun abin da ya dace a yi kafin maganar fara gudanar da harkokin kasuwanci a kogunan.

Kwararren harkar tekun ya kara da cewa babu wani dan kasuwa da zai yi kasadar zuba kudinsa ko kayansa ko kuma jirgin dakon kayansa a kan kogunan ba tare da samun tabbacin tsaro daga Sojin Ruwan Najeriya ba.

“Sojojin Ruwan Najeriyan za su gudanar da nazari a matakai uku. Na farko za su yi shi ne daga Baro zuwa Burutu sannan na biyu shi ne wanda ake gudanarwa. Sannan masu ruwa-da-tsaki za su tattauna a kan kowane rahoton nasu inda za su ba da shawarwarin abin da ya kamata a yi kuma a sa-ido wajen aiwatar da su,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa an kuma tsara taron masu ruwa-da-tsaki domin musayar yawu a kan rahoton farko da makamantansa inda ake sa ran Babban Sakataren Hukumar, Mista Emmanuel Jime, wanda lauya ne, zai jagoranta a watan Satumba a Abuja.

A daya bangaren, Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ce lallai ne a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da an dauki matakan da za su sa jiragen ruwa su fara zirga-zirga a Kogin Kwara, yana mai cewa in ayyuka sun kankama wajen zai samar da ayyukan yi sama da miliyan biyu.