✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina aka kwana shekaru 7 bayan kafa kungiyar #BringBackOurGirls?

An kafa kungiyar ne dai a rana mai kamar ta yau a shekarar 2014, da zummar matsa lamba ga gwamnati kan ceto 'yan matan.

A ranar Juma’a, 30 ga watan Afrilun 2021 kungiyar nan mai fafutukar ganin an ceto ’yan matan Makarantar Sakandiren Gwamnati dare Chibok a jihar Borno take cika shekaru bakwai da kafuwa.

An kafa kungiyar ne dai a rana mai kamar ta yau a shekarar 2014, da zummar matsa lamba ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin an gaggauta ceto ’yan matan wadanda Boko Haram ta sace sun tsaka da rubuta jarrabawar kammala sakandire ta WAEC.

Sai dai a tsawon wadannan shekarun bakwai, har yanzu tsugune ba ta kare ba, sakamakon akwai ’yan mata sama da 100 dake hannun ’yan ta’addan na Boko Haram.

Wasu daga cikin 'Yan matan Chibok din da Boko Haram ta sace
Wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok din da Boko Haram ta sace

A shekarar ta 2014 dai, daruruwan mata ne suka gudanar da wani gagarumin gangami a manyan titunan Abuja, suna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin da ya dace domin ceto ’yan matan da yawansu ya kai 276 a lokacin.

Wannan dai ita ce zanga-zanga ta farko da kungiyar ta jagoranta a wancan lokacin, wacce kuma ta haifar da kungiyar ta #BringBackOurGirls daga bisani.

A karon farko dai, al’ummar garin na Chibok mazauna Abuja ne suka gudanar da zanga-zangar a filin taro na Eagle Square dake Abuja, amma daga bisani ’yan sanda suka tarwatsa su.

Daga cikin ’yan mata 276 da aka sace, 57 sun tsere, 107 kuma aka kubutar da su, yayin da 117 kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

Ko da yake a yanzu ba a jin amonta kamar a ’yan shekarun baya, kungiyar ta sha alwashin ci gaba da fafutuka har sai an ceto dukkan yan matan daga hannun ’yan ta’addan.