✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ina da basira da jajircewa, ku taimaka ku zabe ni’

Tinubu ya ce wakilan APC a Kano ba za su yi nadamar zabensa ba.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma mai neman takarar shugaban kasa a APC, Bola Ahmed Tinubu, ya shaida wa wakilan jam’iyyar a Jihar Kano, cewar yana da basira, hazaka da kuma jajircewar da zai iya shugabancin Najeriya. 

Tinubu, ya bayyana haka ne yayin da ya gana da wakilan jam’iyyar APC a Kano a daren Alhamis, inda ya ce jam’iyyar a Kano ba za ta yi nadamar zabar shi a matsayin dan takarar shugaban kasa ba.

Har wa yau, ya ce idan aka zabe shi zai magance matsalar rashin tsaro, ya bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ya kuma samar wa manoma hanyoyi kawo amfanin gonakinsu zuwa kasuwa.

“Ina kira gare ku da ku goyi bayan burina na zama shugaban kasa ta hanyar ba ni damar samun tikiti a zaben fidda-gwani mai zuwa.

“Yau ce ranar da na zo neman goyon bayanku don zama shugaban Najeriya; Za ku iya cika min burina ta hanyar ba ni kuri’unku.

“Na yi imanin ina da fikira, hazaka da jarumtaka, kada ku yi kuskure, ku yi zabe cikin hikima, ku zabe ni, ina rokon ku don ba zan bari ku taba yin nadamar goyon bayana ba.

“Musayar kayayyaki ita ce tabbatar wa manoma cewa akwai kasuwa ga duk kayan amfanin da suka noma,” a cewar Tinubu.

A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce Tinubu ya yi aiki tukuru domin ci gaban Jam’iyyar APC a Najeriya.

“’Yan Najeriya na burin samun dan takarar da ya fahimci kalubalen da al’ummar kasar nan ke fuskanta kuma wanda ya kware wajen sakuya fasalin kasar,” in ji Ganduje.