✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ina da kwarin gwiwar mace za ta iya gadon Buhari a mulkin Najeriya’

Amina Mohammed ta kalubalanci mata kan su kara jajircewa wajen ganin sun karbi ragamar shugabancin Najeriya idan shugaba Muhammadu Buhari

Mataimakiyar Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed ta kalubalanci mata kan su kara jajircewa wajen ganin sun karbi ragamar shugabancin Najeriya idan shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.

Amina wacce ke jagorantar manyan jami’an majalisar dake wata ziyarar aiki a Najeriya ta bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja.

Tun da farko dai sai da tawagar ta gana da shugaba Buhari a fadar sa ta Aso Rock inda suka tattauna a kan hanyoyin sake gina kasar bayan mummunar illar da annobar COVID-19 ta yi mata.

Amina, wacce tsohuwar Ministar Muhalli ce a Najeriya  ta ce dole ‘yan Najeriya su tashi tsaye wajen gina kasa ba tare da la’akari da banbance-banbancensu na siyasa ba.

Ta ce, “Ya kamata mu fahimci abinda yake daidai domin muga ya faru, a rukuninmu ko a daidaikunmu. Akwai bukatar girmama kowanne bangare na kasarmu saboda kowa na da irin gudunmawar da zai bayar wajen gina kasa.”

Da aka tambayeta ko tana da sha’awar tsayawa shugabancin idan Buharin ya kammala mulki sai ta ce, “Wannan shine fata na, bana tunanin mace ba za ta iya ba. Na yi amannar cewa duk wanda ya yi kokari zai iya cimma burinsa.

“Saboda haka dole mata su tashi tsaye. Suna da kusan kaso 50 cikin 100 na kuri’un da ake kadawa, idan har za su iya neman goyon bayan maza, me zai hana su cimma burinsu? Ban ga dalilin da zai sa ace mace ba za ta mulki Najeriya ba.

“Hakikanin wanda muke bukata a Najeriya shine wanda zai kaimu tudun mun-tsira ta hanyar tabbatar da hadin kan kasa da ciyar da ita gaba.

“Sai mun motsa daga magana da baki kawai zuwa aiwatarwa a aikace a dukkan kananan hukumomi 774, jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. Wannan shine aikin da ake da bukatar yi kuma za a iya yi a karkashin shugabancin mace,” inji Amina.

Jawaban nata na zuwa ne daidai lokacin da mace ‘yar Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ke hankoron darewa kujerar shugabancin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO) a matsayin mace ta farko.

Ba kasafai dai ake samun mata su yi shugabanci a nahiyar Afirka ba, in banda a kasar Saliya da Elen Johnson Sirleaf ta kafa tarihin zama mace ta farko da ta shugabanci wata kasa a nahiyar daga shekarun 2006 zuwa 2008.