✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina goyon bayan dawo da Bundesliga —Ministan Jamus

Ministan harkokin cikin gida da wasanni na kasar Jamus, Horst Seehofer, ya bayyana goyon bayansa ga dawowar gasar kwallon kafa ta Bundesliga a cikin watan…

Ministan harkokin cikin gida da wasanni na kasar Jamus, Horst Seehofer, ya bayyana goyon bayansa ga dawowar gasar kwallon kafa ta Bundesliga a cikin watan Mayu duk da annobar coronavirus a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa Horst Seehofer ya fadi hakan ne ranar Lahadi lokacin da yake hira da jaridar Bild kwanaki uku kafin hukumomi a kasar su gudanar da wani taro a kan lamarin.

“Na ga tsare-tsaren da Hukumar Kula da Gasar Kwallon Kafa ta Jamus ta yi kuma ya yi kyau; hakan ya sa nake goyon bayan dawo da wasanni a watan Mayu,” inji Mista Seehofer.

Hukumar Kula da Gasar Kwallon Kafa ta Jamus dai ta goyi bayan dawo da wasanni wadanda za a rika bugawa ba tare da halartar ’yan kallo ba a tsakiyar watan Mayu.

Idan hakan ya kasance, Jamus za ta zama kasar Turai ta farko ta da dauki irin wannan matakin.

Ministan ya kuma bukaci a samu fahimtar juna tsakanin kungiyoyin kwallon kafa da ’yan wasa a kan ka’idojinda za a gindaya.

“Idan aka samu wanda ya harbu da cutar a wata kungiya, baki daya kungiyar da ’yan wasa da ma ma’aikatan horaswa za su killace kansu na sati biyu”, inji shi.

Ya kara da cewa ba za a bai wa kungiyoyin wasan wani tsarin gwaje-gwaje na musamman ba duk da bukatar da wasu daga cikinsu suka gabatar cewa a yi wa ’yan wasansu gwaje-gwaje a kai a kai.