✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina kudaden da aka kwato suke? Sarkin Musulmi ga Gwamnati

Sarkin Musulmi ya ce jazaman ne a yi bayanin inda kudaden suke da abin da aka yi da su.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi bayanin inda kudaden satar da ta kwato suke da kuma abin da ta yi da su.

Sarkin Musulmi ya bukaci haka ne a ranar Talata, yana mai cewa rashin yin bayani game da dukiyoyin da aka kwato zai iya haifar da matsala.

“Wajibi ne gwamnati ta yi wa ’yan Najeriya bayani saboda muna so mu  san biliyan nawa aka kwato daga hannun tsofafffin shugabannin. Ina kudaden suke kuma me ake yi da su?

“Yin wannan bayani ya zama wajibi, idan aka yi la’akari da yadda bangaren ilimi da saura bangarori kamar hanyoyi ke matukar bukatar kulawar gwamnati,” inji Sarkin Musulmi.

Ya yi bayanin ne a taron tattaunawar masu ruwa da tsaki kan Manufofin Da’a na Kasa, wanda Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya shirya, da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da dangoginsa (ICPC) na shiyyar Arewa-maso-Yamma.

Sarkin Musulmi, wanda Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya wakilta, ya ce Daular Sakkwato ta wallafa litattafai da dama a kan rashawa da kuma yadda za a magance ta a Musulunce.

Don haka ya bukaci ’yan Najeriya su nemi litattafan domin samun ilimin magance matsalar cin hanci da ta yi wa Najeriya katutu.

Shugaban Ofishin ICPC mai kula da Jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, Ibrahim Alkali, ya ce bullo da Manufofin Da’a na Kasa ya zama dole “ana kuma aiwatar da su ne da nufin maido da nagarta da rikon amana wadanda suka yi karanci a kasar a halin yanzu.”

Kudaden da aka kwato na cikin kasafi —Malami

Kazalika a ranar Talata, Kwamitin Binciken Wucin Gadi da Majalisar Wakilai ta kafa kan kudade da kadarorin sata da aka kwato daga 2002 zuwa 2020, ya nemi bayanansu daga Akanta-Janar na Kasa, Ahmed Idris.

A lokacin zaman, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana wa Kwamitin cewa: “An sanya duk kudade da kadarorin a Asusun Babban Bankin Najeriya (CBN) na Ajiyar Kadarorin Gwamnati da Aka Kwato kuma CBN ya tabbatar da karbar su da kuma yawansu.

“Abubuwan da aka kwato da ma sauran kudade na daga cikin kudaden da ake yin kasafin kudi da su, da amincewar Majalisar Tarayya.”

Nasarar kwato kadarorin gwamnati

Malami ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta samu nasarori a bangaren kwato dukiyoyin gwamnati da aka sace.

Ya ce: “A watan Disamban 2017 mun yi nasarar kwato Dala miliyan 322 daga kasar Switzerland, daga cikin abin da ake kira Kudaden Abacha.

“A Mayu 2020, mun kwato Dala miliyan 311.8 daga Tsibirn Jersey da Birtaniya.

“Oktoba 2020 kuma mun kwato Yuro miliyan 5.5 na Kudaden Abacha daga Northern Ireland sannan a watan Mayun 2021 mun kwato Fam miliyan 4.2 na kudin Ibori daga Birtaniya,” inji Malami.

Daga Sagir Kano Saleh, Abubakar Auwa, Sakkwato da Balarabe Alkassim.