✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane sun sha mamakin yadda na zama dan bindiga —Bello Turji

Ba na yi wa mata fyade.

Kasurgumin dan bindigar nan na Jihar Zamfara, Bello Turji, wanda ya shahara wajen garkuwa da mutane ya bayyana cewa mutane sun sha mamakin yadda ya zama dan bindiga.

Bello Turji, wanda ake zargi da yawancin ta’asar da ake aikatawa a yankin Arewa maso Yammacin kasar, ya  bayyana hakan ne a cikin hirar gaba-da-gaba da mataimakin editan jaridar  Daily Trust, Abdulaziz Abdulaziz da su kayi a kwana nan.

A cewarsa, mutane da dama a shekarun baya idan aka ce masu zai zama shahararren dan bindiga, musamman sarkin shinkafi wanda shine sarkin mahaifar Turji ba za su yarda ba.

Ya ce a lokutan baya yana zuwa wurin sarkin Shinkafi kuma shima sarkin Shinkafi ya san shi, kuma yana zuwa har gurinsa suna gaisawa.

Har ila yau, ya ce a wancan lokacin idan aka ce zai zama rikakken dan bindiga shi ma ba zai yarda ba, saboda kowa yasan su a wancan lokacin su ba barayin shanu ba ne Fulani ne kawai kiwo suke yi, amma abin da ake masu ne ya sa suma dole suka sauya.

Ya kara da cewa, ayyukan ‘yan sa kai na daga cikin abubuwan da suka kara ta’azzara wannan rikici na ’yan bindiga tare da tursasa shi da sauran matasa zama ’yan ta’adda.

Ba na yi wa mata fyade

Don gane da zargin cewa kuma yana yi wa mata fyade, ya ce mutane ne kawai ke fadin son zuciyarsu.

Turji ya ce kowa na iya fadin abin da ya ga dama, amma abin da ya sani shi ne, shi ba ya fyade, yana mai cewa akwai mata a inda yake.

Ya ce da yana fyade, da ya fara da matan da ke inda yake a yanzu haka.

“Idan mata ne ai gasu nan ba sai na je na yi garkuwa da su ba tukunna zan yi amfani da su.

“Yanzu duk laifukan fyaden da ake samu misali a Kano nan ma Turji ne, to ka gani wannan ai ba sai an yi wa mutum wani karin bayani ba”