✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan iya barin Barcelona ba —Messi

Dan wasan da ya fi yawan kwallo a Barcelona ya fadi dalilinsa na zama a kungiyar

Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya tabbatar da ci gabansa da zama a kungiyar, ‘yan kwanaki bayan dambarwa kan barinsa kungiyar.

Messi wanda ya fi kowa yawan cin kwallo a Barcelona ya ce zai ci gaba da zama zuwa cikar wa’adin da ba sai ya biya Yuro miliyan 700 da ke cikin yarjejeniyarsa da kungiyar ba.

Messi ya ce ba zai yiwu wata kungiya ta iya biyan kudin ba domin ta saye shi, kamar yadda kwantaraginsa ya shardanta biyan Barcelona Yuro miliyan 700 kafin ya bar ta.

An yi ta maganganu cewa wasu kungiyoyi na neman sanyen dan wansan, amma sharadin da ke cikin kwantaraginsa ya kawo cikas.