✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina neman goyon bayanku don cikar burina —Tinubu ga Sanatocin APC

Tinubu ya roki sanatocin da su yi la'akari da gogewarsa da kuma cancantarsa.

Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roki sanatocin jam’iyyarsu da su mara mishi baya don cikar burinsa na zama shugaban kasar Najeriya.

Tinubu ya yi wannan roko ne a ranar Laraba, yayin wani zama da ya yi da sanatocin APC a Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja.

Tinubu ya nemi hadin kan sanatocin, inda ya ce, “Ku mara min baya saboda irin gogewar da nake da ita.

“Kun san abin da ya sa na zo nan? Na zo ne domin neman shawarwari, hadin gwiwa da kuma kuma taimako.

“Najeriya tana gabar da take bukatar canji, ga shi kuma shugaban kasa yana dab da kare wa’adinsa na biyu.

“Zabe da kuma babban taron jam’iyyarmu na nan zuwa, saboda haka nake neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa.

“Ba zan taba iya samu ba idan har na zauna a gida.

“Amma na ina da yakinin idan muka hada karfi tare za mu iya cim ma nasara.

“Ina fatan za ku mara min baya don cikar burina.

“Masu iya magana na cewa, idan kana so ka yi sauri, to ka tafi kai kadai, amma idan kana so ka je da nisa, to ka tafi tare da jama’a.

“Ina son hadin kan kowa don jam’iyya ta tsayar da ni a matsayin dan takarar shugaban kasa.

“Ina rokon ku, ku yi la’akari da gogewa ta da kuma cancanta ta,” inji Tinubu.