Ina son barin Najeriya cikin kwanciyar hankali a 2023 —Buhari | Aminiya

Ina son barin Najeriya cikin kwanciyar hankali a 2023 —Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
    Abubakar Muhammad Usman

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce fatansa shi ne ya kammala mulkin Najeriya, ya bar a cikin kwanciyar hankali a 2023.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin kasa (NTA), ya yi da shi da dare a ranar Juma’a.

  1. Sule Lamido da Saraki sun yi ganawar sirri da Obasanjo
  2. Buhari ya mika karin kasafin biliyan N895 ga Majalisa

Buhari ya jaddada cewa zai sauka daga kan mulki a 2023 ba tare da neman wa’adin mulki na uku ba.

Kazalika, ya ce samun nasarar gwamnatinsa zai ta’allaka ne ga ci gaban jam’iyyar APC bayan zaben 2023.

Matsalar tsaro

Ya nanata aniyar gwamnatinsa na ci gaba da yaki da ta’addanci da ya kunshi yakar ’yan bindiga a fadin Najeriya.

Sannan ya ce ba daidai ba ne a yi zargin cewa rashin kauna ce matakin da jami’an tsaro ke dauke a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, musamman kan haramtacciyar ’yan kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya.

“Mun tura ’yan sanda da sojoji Arewa don su yaki ’yan bindiga,’’ cewar shugaba Buhari.

Da yake bayyana ci gaban da aka samu a bangaren tsaro daga shekarar 2015, Buhari ya ce gwamnatinsa na fuskantar kalubale kan makamai ke shiga hannun mutane ba bisa ka’ida ba.

Ya jadadda cewar abu na farko da ya fi maida hankali a kai shi ne magance matsalar tsaro, domin idan babu tsaro, to babu yadda za a yi mutane su shigo Najeriya don zuba dukiyarsu.

Har wa yau, ya yi Allah wadai da tarzomar da zanga-zangar #EndSARS ta haifar, yana mai cewa hakan na iya hana masu saka jari ko ’yan kasuwa daga wasu kasashe shigowa Najeriya.

Yaki da cin hanci

Buhari ya ce yaki da cin hanci karkashin mulkin dimokuradiyya na da matukar wahala duba da yadda ake tafiyar wahainiya kan lamarin.

“Yana da matukar wahala yaki da cin hanci a kan wannan tsarin. Lokacin da nake matashina, na kama ’yan siyasa na daure su har sai da aka tabbatar da cewar ba su da laifi,” a cewarsa.

Sannan ya ce mutane da dama sun aminta da yadda gwamnatinsa ke kokari duk da tarin kalubale da take fuskanta.

Shugaban Kasar ya bukaci a gina sabbin kotuna shari’ar cin hanci, don taimakawa wajen yaki da shi cikin sauki.