✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina tallan doya don tsare mutuncina —Gurgu

Da tallan doyar da nake yi sai duk ’ya’yan yi karatu a jami’a

Wani mai kafa daya da ke tura baro yana tallar doya a ciki ya bayyana cewa yana yin haka ne domin kare mutuncinsa a matsayinsa na magidanci. 

Malam Abdullahi Abubakar da ke garin Gombe ya ce yin bara ko dogaro da wani bai dace da shi ba a matsayin magidanci kuma uba, don haka ya rungumi tallar doya a matsayin sana’a.

“Nakan tafi ina tsalle (ina dogara sanda ina kuma tura baro) tun daga karfe shida na safe zuwa shida yamma ina tsalle ina talla.

“Ina yin tafiya mai nisa zuwa duk inda ta kama saboda ba na son raggwanci kuma ba na jin kunya saboda ai sana’ata ke nan,’’ inji shi.

Ya kara da cewa bai dace ba don mutane na da nakasa sai su rika fakewa da lalurar wajen yin barace-barace.

Ya ce, “Yana kyau mutum ya nemi na kansa ya kuma kare mutunci da kimarsa; amma idan ka je kana rokon mutane za a raina ka.

“Kullum ina samun kwarin gwiwa saboda dana da kuma bukatar ba wa iyalina cikakkiyar kulawa, duk da cewa wani lokaci nakan gaji kwarai saboda aikin da na yi kafin ranar.

A hirar da aka yi da shi ranar Juma’a, magidancin ya ce yanzu ya shekara biyu yana sayar da doya.

“Nakan samu kimanin N3,000 a kullum kuma ina amfani da kudin da na samu wajen hidimar iyalina a matsayina na maigida.’’

Da aka tambaye shi game da matasa masu yin bara  ko maula,  sai Abubakar ya kada baki ya ce yawancinsu ba su hakurin yin karamar sana’ar da babu kudi a cikinta sosai.

“Sun fi son sana’ar da za ‘su sha kwana’ su kudance cikin da kankanin lokaci.

“Ko ba yawa kake samu kana kare mutuncinka, sai Allah Ya cika maka burinka ba ba ka nutsuwa a nan gaba, tare da tabbacin samun abin da kai da iyalanka za ku ci,’’ inji shi.

Abubakar wanda ke da daya a halin yanzu ya ce yana da burin samun karin wasu biyu, kuma kowannensu sai ya yi jami’a in Allah Ya yarda.

Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe da masu hari da su taimaka masa ya mallaki shago domin ya fadada sana’ar tasa.

“Bin tituna da unguwanni ina tsalle daga karfe shida na safe zuwa shida na yamma ba abu mai sauki ba ne, amma dole in yi saboda iyalina. Amma ina tunanin yanayin rayuwa nan gaba.

“Da zan samu shago in fadada sana’ata da zan samu damar hutawa da kuma abin da zan tara domin cika burin da nake da shi wa ’ya’yana,’’ inji shi.