✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina tare da El-Rufa’i kan ragargazar ’yan ta’adda —Tinubu

Tinubu ya ce akwai bukatar hada kai don yakar ’yan bindiga

Jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana goyon bayansa game da kalaman Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i na cewar a yi wa dazukan da ’yan bindiga ke ciki ruwan bama-bamai.

Tinubu ya ziyarci Kaduna ne a ranar Talata don jajanta wa jama’ar jihar kan hare-haren ’yan bindiga da ya addabe su, musamman a baya-bayan, wanda ’yan bindigar suka dasa wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna bam.

Ya yi kira da cewar ya kamata a hada hannu tsakanin gwamnati da jami’an tsaro don ganin an kawo karshen ayyukan ta’addanci.

Tinubu, ya yi karin haske game da kalaman El-Rufai, inda ya ce akwai bukatar yin duk abin da ya dace don ganin bayan ’yan bindigar.

“Ni ba masanin harkar tsaro bane, amma ina bayansa, ina tare da shi kan yadda za a yi jami’an tsaro su kawo karshen ta’addancin ’yan bindiga,” a cewar Tinubu.

Ya kuma ce duk wani yanki da aka kai wa hari tamkar an kai wa Najeriya ne baki daya, wanda a cewarsa akwai bukatar hada kai waje daya don amfani da duk hanyar da ta dace don ganin an kawar da ta’addanci.

Tinubu ya roki ’yan Najeriya da su tallafa wa mutanen da hare-haren ’yan bindiga ya shafa a Jihar, duba da irin halin matsin rayuwar da ake fama da shi.

“Na zo ne don jajanta wa gwamna Nasir El-Rufa’i da jama’ar Kaduna kan harin jirgin kasan da ya faru. Harin ya shafi kasa baki daya kuma ya shafi dukkaninmu.”

Tshohon Gwamnan na Legas ya kuma ba da tallafin Naira miliyan 50 ga wadanda harin ya ritsa da su.

Yayin ziyarar dai, Tinubu ya samu rakiyar Gwamnan El-Rufa’i da Sanata Kashim Shettima inda ya ziyarci wadanda harin na Kaduna ya ritsa da a asibiti.