✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina umartar dakarun Najeriya da su shafe ’yan ta’adda daga doron kasa —Buhari

Shekaru 12 da suka wuce sun kasance cike da kalubale, ganin barazanar tsaro iri iri da suka addabi kasar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya umurci dakarun kasar da su tunkari ’yan ta’adda su kuma shafe su daga doron kasa.

Shugaba Buhari ya ba da wannan umurni ne ranar Alhamis yayin bikin yaye hafsoshin soji 247 a garin Jaji da ke Jihar Kaduna da suka halarci kwas na 44.

Ya ce shekaru 12 da suka wuce sun kasance cike da kalubale, ganin barazanar tsaro iri iri da suka addabi kasar.

A cewar shugaban kasar, matsalolin tsaron da suka addabi duniya iri daya ne, saboda sun kunshi kungiyoyi dabam dabam masu daukar makamai a yankuna daban-daban.

Buhari tare da manyan baki da kuma hafsoshin soji 247 da aka yaye a garin Jaji.
Buhari yayin da ya halarci bikin yaye hafsoshin soji 247 a garin Jaji.

Shugaban Najeriyan ya ce kungiyoyin ta’addanci da na ‘yan bindiga da dama su na cikin kasar, kuma abin da ya dace shine a tinkare su a shafe su daga doron kasa don kawo zaman lafiya.

Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bada gudummawar da ta dace don tabbatar da samun sakamakon da ake bukata.