✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Indiya na fama da matsanancin zafi a tarihi

Shekara 10 da suka wuce sun kasance mafiya munin yanayin zafin da kasar Indiya ta fuskanta a tarihi yayin da ofishin kula da yanayi na…

Shekara 10 da suka wuce sun kasance mafiya munin yanayin zafin da kasar Indiya ta fuskanta a tarihi yayin da ofishin kula da yanayi na kasar ke alakanta lamarin da dumamar yanayi da duniya ke fuskanta – wanda hakan ya haddasa mutuwar fiye da mutum 1,500 a bara kawai.

Indiya, wacce take da yawan jama’a biliyan 1.3, tana kan gaba wajen fuskantar illar sauyin yanayi inda take fama da ambaliyar ruwa mai munin gaske da karancin ruwa tare da zafi na fitar hankali.

Birnin Chennai da ke Kudancin kasar a bara ya yi shelar ‘kafewar ruwan famfo kaf’ a fadin birnin.

Yanayi daga shekarun 2010 zuwa 2019 ya kasance kan digiri 0.36 a ma’aunin Celsius (0.65 digiri na ma’aunin Fahrenheit) wanda ya gota matsakaicin mizani a tsawon lokaci, kuma mafi muni a zafi a tarihi tun daga 1901 da aka fara adana bayanai, kamar yadda Hukumar Kula da Yanayi ta Kasar ta sanar a farkon makon nan.

Cikin wadanda suka rasa rayukansu mutum 850 sun rasu ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliya. Sai kuma wadansu 350 da suka rasu dalilin zafi da ya kai maki 51C (123.8F). Sai kuma wadansu 380 da tsawa da walkiya da ruwan sama suka hallaka su.