✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Indiya za ta sayi man fetur daga Rasha a farashi mai rahusa

Indiya ta ce ta shirya sayen man fetur din tare da wasu albarkatun Rasha.

Rahotanni sun bayyana cewa Indiya ta soma duba yiwuwar sayen man fetur da wasu albarkatu daga kasar Rasha a farashi mai rahusa.

Wannan na zuwa ne a yayin da kasashen Turai ke ci gaba da kakaba takunkumai ciki har da kaurace wa sayen man fetur din kasar a sakamakon mamayar da dakarun Rashar ke yi a Ukraine.

Kasar Indiya na sayen kashi 80 cikin 100 na dukkan albarkatun man fetur daga kasashen waje ne, kuma a ciki tana sayen kimanin kashi biyu zuwa kashi uku cikin 100 na albarkatun man daga Rasha.

Ta na bukatar man na Rasha ne saboda farashin mai na tashin goron-zabi a kasuwannin duniya, gwanatin Indiya na bukatar rage yawan kudin da ta ke kashewa kan makamashi.

Wani jami’in gwamnatin Indiya, ya ce kasar na farin cikin sayen man na Rasha kuma ba ta damu da barazanar takunkumi da kasashen yammacin duniya ke yi wa dukkan wadanda suka yi hulda da Rasha ba.

Indiya ta ce aiki ya yi nisa kan samar da wani tsari na sauya takardun kudin kasashen biyu wato daga Rupee zuwa Ruble.