✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta amince da kara wa’adin sabunta rajistar zabe

Kwamitin Zabe na Majalisar Wakilai ne ya sanar da haka

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta amince da kara wa’adin yin rajistar katin zabe.

Shugabar Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin Zabe, Aisha Dukki ce ta bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Laraba.

A baya dai hukumar ta sanya ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta rufe sabunta rajistar.

Sai dai kiraye-kirayen da ake mata na kara wa’adin bisa fitowar dafifi da ‘yan Najeriya sukai domin mallakar rajistar ya sanya ta amsa kiran.

Yanzu haka dai bayan kwamitin zaben majalisar ya gana da Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, sun amince da kara wa’adin ya dara ranar 30 ga watan Yunin 2022 da majalisar ta bukata.

A hannu guda kuma, shugabar ta ce duk da hukumar zaben ta amince da bukatar majalisar ta kara wa’adin, ba lallai ta kara shi kamar yadda majalisar ta bukata ba, sai dai za su koma su tattauna mafita kafin sanar da wa’adin da za su iya karawa.

To sai dai wata majiya daga hukumar zaben ta ce da wuya a iya kara wa’adin da zai dara 30 ga watan Yunin, kuma da yiwuwar hukumar ta daukaka kara kan dakatarwar da kotu ta yi mata na rufe sabunta rajistar a ranar 30 ga watan Yunin.

“Lamarin zai shafi jadawalin zaben 2023, tunda dole sai mun buga katinan wadanda suka yi rajistar, ka ga hakan na nufin sai mun matsar da zaben kansa ke nan,” inji majiyar.