✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta ayyana zaben Anambra a matsayin wanda bai kammala ba

Hukumar ta ce sai an sake zaben a Karamar Hukumar Ihiala kafin ta ayyana wanda ya lashe.

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ayyana zaben Gwamnan Jihar Anambra na ranar Asabar a matsayin wanda bai kammala ba.

Jami’ar hukumar da aka dora wa alhakin sanar da sakamakon, Farfesa Florence Obi ce ta bayyana hakan da sanyin safiyar Litinin a hedkwatar hukumar da ke Awka, babban birnin Jihar.

Ta ce zaben ya gaza kammala ne sakamakon rashin gudanar da shi a Karamar Hukumar Ihiala ta Jihar.

A cewarta, dogaro da tanade-tanaden Dokar Zabe ta Kasa, za a sake gudanar da zaben a Karamar Hukumar ranar Talata.

Ta ce, “Ni Farfesa Florence Obi, ina amfani da damar da aka bani a matsayin mai bayyana sakamakon zabe wajen dakatar da ci gaba da tattara sakamakon, har sai an sake gudanar da zabe a wasu mazabu 320 da ke Karamar Hukumar Ihiala.

“Za a gudanar da zaben ne ranar Talata, tara ga watan Nuwamban 2021,” inji ta.

Dan takarar jam’iyyar APGA, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Farfesa Charles Soludo ne dai yake kan gaba a zaben na ranar Asabar.

Soludo ya sami kuri’a 103,946, sai Valentine Ozigbo na PDP da ke biye masa baya da kuri’a 51,322, yayin da Andy Uba na APC ya zo na uku da kuri’a 42,942.

Jimlar mutanen da suka yi rajistar zabe a Jihar sun kai 246,638, yayin da 241,090 kuma aka tantance su a zaben.

Kazalika, jami’ar ta INEC ta ce yawan kuri’un da aka kidaya sun kai 229,521, sai kuma guda 7,841 da suka lalace.