✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

INEC ta bude shafin duba sakamakon zabe ta intanet

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bude shafi na intanet da za a rika amfani da shi wajen duba sakamakon zabe domin ingantawa tare da…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bude shafi na intanet da za a rika amfani da shi wajen duba sakamakon zabe domin ingantawa tare da yin komai a fili.

Kwamishinan hukumar mai kula da yada labarai da wayar da kan jama’a, Festus Okoye ya ce shafin zai fara aiki daga Asabar 8 ga watan Agusta a zaben cike gurbi na Mazabar Nasarawa ta Tsakiya.

Ya ce harkar tafiyar da sakamakon zabe ya kasance daga cikin manyan kalubalen harkar zabe a Najeriya kuma “INEC ta kosa ta rika yin komai a fili a harkar zabe n Najeriya, musamman wajen bayyana sakamako.

“Babban ginshikin demokradiyya ne a kidaya kuri’u yadda ya kamata, wanda shi ya sa muka kirkiro Form EC 60E, wanda kamar kwafi ne Form EC 8A wanda za a rika likawa a wajen zabe”, inji Festus.

Sai dai ya ce duk da hakan, akwai bukatar kara inganta harkar tafiyar da sakamakon zaben, wanda shi ya sa INEC ta kirkiro da shafin intanet da jama’a za su iya duba sakamakon mai suna IReV.

INEC ta ce IReV zai ba jama’a damar duba sakamakon zaben tun daga matakin mabaza da zarar an kammala kada kuri’a.

Festus Okoye ya ce sabon shafin zai fara aiki ne daga zaben cike gurbi da za a yi a mazabar Nasarawa ta Tsakiya a Majalisar Dokokin Jihar ta Nasarawa ranar Asabar 8 ga watan Agusta.