✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta cire Mohammed Abacha daga jerin ‘yan takarar Gwamnan Kano

Wannan shi ne abin da hedikwatar INEC da ke Abuja ta dawo mana da shi.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta cire sunan Mohammed Abacha daga jerin ‘yan takararkarun gwamnan Jihar Kano.

Sunan Mohammed Abacha ya bace a jerin sunayen ‘yan takarar da INEC ta fitar da za su kara a zaben kujerar gwamnan Kano a badi.

Wannan dai ta bayyana ne a ranar Juma’a yayin da INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarkarun da za su kara a zaben mai zuwa, inda aka nemi sunan dan tsohon Shugaban Najeriya, Marigayi Janar Sani Abacha.

Hukumar ta musanya sunan nasa da na Sadiq Muhammad Wali, dan tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Aminu Wali.

Sauran ‘yan takarkarun da suke cikin jerin sunayen sun hada da na Mataimakin Gwamna mai ci, Nasir Yusuf Gawuna da abokin takararsa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Murtala Sule Garo.

A cikin jerin sunayen ’yan takarar, akwai Abba Kabir Yusuf da abokin takararsa, Aminu Abdussalam a karkashin jam’iyyar NNPP.

Sai kuma Salihi Tanko Yakasai na jam’iyyar PRP.

Wannan sauyin na zuwa ne duk da cewa a baya INEC ta furta cewa zaben sharar fage da aka yi na Mohammed Abacha shi ne sahihi ta kuma bashi takardar lashe zabe.

Da yake mayar da martani kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na INEC reshen Jihar Kano, Ahmad Adam Maulud, ya ce hukumar a matakin jiha ta mika abin da sakamakon zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata ya tabbatar zuwa ga hedikwatar ta kasa.

Sai dai ya ce wannan sunayen da aka gani hukumar ta manna a bango ranar Juma’a shi ne abin da aka dawo musu da shi  daga hedikwatar hukumar da ke Abuja.

“Mun aika da abin da muka yi zuwa hedkwatarmu ta kasa kuma abin da muka lika a yau [Juma’a] ya fito daga gare su kai tsaye.”

“Duk wanda ke son neman karin haske ya tuntubi hukumar jam’iyyarsa ta kasa don samun bayanai,” kamar yadda kakakin INEC din ya shaida wa Aminiya.