✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

INEC ta dage zaben gwamnoni

INEC ta dage zaben da mako guda saboda kurewar lokacin sanya bayanai a na'urar BVAS

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage zaben gwamnoni da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 11 ga watan Maris da muke ciki.

Ma’ajiyar Aminiya a INEC da ta nemi a boye sunanta, ta bayyana cewa hukumar ta yanke shawarar dage zaben da mako guda saboda kurewar lokacin da za ta iya sanya bayanan zaben gwamnoni da ’yan majalisun jiha a na’urar BVAS.

Kawo yanzu dai INEC ba ta ba fitar da sanarwa hukumance ba, amma majiyarmu ta ce ana sa rana gudanar da zaben a ranar Asabar, 18 ga watan Maris da muke ciki.

Ta ce dage zaben ya zame wa Hukumar dole ne saboda ba za ta iya sanya bayanan da ake bukata ba a na’urorin BVAS da ake tantance masu zabe kafin lokacin zaben, ba tare da an samu matsala a zaben ba.

“Ba zai yiwu ba, dole sai an samu matsala, saboda ko BVAS din da ke Jihar Kano kadai ba ’yan  kadan ba ne.

“Sai an kawo su sannan idan aka sanya musu bayanai, a yi musu caji, a tura kananan hukumomi zuwa yankunan zabe.

“Dole a samu matsala idan aka yi a yanzu haka,” in ji majiyar.

Wannan na zuwa ne kwana biyu kafin zaben gwamnoni da ’yan majalisun jihar, kuma a ranar da Kotun Daukaka Kara ta sahale wa INEC sanya bayanan zaben a BVAS.

Majiyarmu a INEC ta shaida mana cewa karar da wasu ’yan takarar shugaban kasa suka shigar na neman bincikar kayayyakin zabe shugaban kasa da ya gudana ranar 25bga watan Fabrairu ne ya kawo tsaikon.

“Tunda suna son bincikar sakamako da kayayyakin zaben ka ga ba yadda za a yi mu taba ko mu goge abin da ake cikin BVAS.

“Wannan shi ne ya janyo jinkirin,” in majiyar tamu.