✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta kara wa’adin karbar katin zabe

INEC ta kara mako guda a kan wa'adin da sanar na kammala karbar katin zabe

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta kara wa’adin da ta sanar na kammala rabon katin zabe da mako guda a fadin Najeriya.

Kwamishinan INEC kan wayar da kai da kuma yada labarai, Festus Okoye, ya ce baya tattaunawa kan batutuwan da suka shafi zabe mai zuwa, INEC ta samu kwarin gwiwa game da yadda mutane suka yi fitar dango wajen karban katun zabensu a fadin Najeriya.

Ya ce, hukumar ta “tsawaita rabon katin zaben da kwana takwas, zuwa ranar Lahadi 29 ga waan Janairu, 2023.

“Yanzu lokacin karbar katin zaben shi ne daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana, har da ranakun Asabar da Lahadi.”

Da farko INEC ta sanya 22 ga watan Janairu a matsayin ranar rufe rabon katunan zaben, wanda ta mayar zuwa cibiyoyin rajistar zabe da kuma gundumomi.

Amma Okoye ya shaida wa manema labarai cewa, “A wasu jihohin an karbi katunan zaben 100,000 a cikin kwana biyar da suka gabata, da aka mayar da rabon zuwa gundumomi da cibiyoyin zabe na yanki.

“A shirye hukumar take domin tabbatar da ganin wadanda aka yi wa rajista a wannan karon sun karbi katunan zabe kafin zaben da ke tafe.

“Wannan ne dalilin da ya ya muka kara wa’adin rufe rabon kain zaben da kwana takwas.”