✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta mika wa Tinubu da Shettima shaidar lashe zabe

Tinubu ya samu kuri’un ya yawansu ya kai miliyan 8 da dubu 794 da 726.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta mika wa Zababben Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima shaidar lashe zabe.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya mika wa Tinubun da Shettima shaidar lashe zaben a Cibiyar Taro ta Kasa ICC da ke Abuja.

Tun a safiyar wannan Larabar Farfesa Yakubu ya sanar da karfe 3 na tsakar ranar yau a matsayin lokacin da zai mika sakamakon lashe zaben ga wadanda suka yi nasara a zaben Shugaban Kasa da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Farfesa Yakubu ya fadi hakan ne yayin da yake ayyana tsohon gwamnan na Jihar Legas a matsayin Zababben Shugaban Najeriya bayan kammala karba da tattara sakamakon zaben a Cibiyar Taro ta Kasa ta ICC da ke Abuja.

Shugaban na INEC da ke bayar da sanarwar alkaluman zaben, ya ce Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’un ya yawansu ya kai miliyan 8 da dubu 794 da 726.

Alkaluman INEC sun bayyana Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a matsayin na biyu da yawan kuri’u miliyan 6 da dubu 984 da 520, yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya zama na 3 da yawan kuri’u miliyan 6 da dubu 101 da 533.

Sai kuma Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya zo na 4 da yawan kuri’u miliyan 1 da 496 da 687.

Nasarar Bola Tinubu a zaben na Najeriya na zuwa ne bayan lashe fiye da kashi 25 na kuri’un da aka kada a jihohin Najeriya 30 yayin zaben ranar 25 ga watan Fabarairu.

Jerin jihohin da Tinubu ya lashe a zaben shugaban kasar sun hada da jihar Rivers da Borno da Jigawa da Zamfara da Benuwe da Jihar Kogi baya ga Kwara da Neja da kuma Osun kana Ekiti da Ondo da Oyo da Jihar Ogun.

A bangare guda, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya lashe zaben jihohin Katsina da Kebbi da Sokoto da Jihar Kaduna baya ga Gombe da Yobe da Bauchi da kuma Adamawa kana Taraba.

Sauran jihohin da ya lashe zaben sun hada da Osun, da Akwa Ibom da kuma Bayelsa.

A bangare guda, Peter Obi ya lashe jihohin Edo da Cross River da Delta da Lagos da Abuja Fadar Gwamnatin Kasar kana Filato da Imo da Ebonyi da Nasarawa da Anambra da Abia da kuma Enugu.

Haka kuma, Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya lashe Jihar Kano ne kadai ko da ya ke ya samu kuri’u a wasu jihohin.