✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta sa ranar zaben Shugaban Kasa na 2023

A yanzu Najeriya tana da kimanin kwanaki 855 kafin babban zaben kasa na gaba.

Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta sanar da ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar zaben Shugaban Kasa da za a gudanar a shekarar 2023.

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoban 2020.

Sanarwar Shugaban Hukumar ta zo ne yayin da ya ke gabatar da sakonsa na fatan alheri yayin rantsar da kwamitin riko na musamman da zai sake yin bita a kan kundin tsarin mulkin kasa na 1999.

A cewarsa, a yanzu Najeriya tana da kimanin kwanaki 855 kafin babban zaben kasa na gaba.