✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta sake kara wa’adin karbar katin zabe

Hukumar ta ce ta yi hakan ne don ta ba mutane damar mallakar katinan nasu

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da kara mako daya a wa’adin daina raba katin zabe, inda za a ciga da karba har zuwa ranar biyar ga watan Fabrairun 2023.

Kwamishinan Hukumar Mai Kula da Wayar da Kan Jama’a, Festus Okoye ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Asabar.

A baya dai, hukumar ta sanya ranar 29 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar karshe ta karbar katin.

Sai dai Okoye ya ce INEC ta yi karin ne saboda ta ba ’yan Najeriya da yawa damar karbar katinan nasu, a daidai lokacin da ya rage kasa da mako hudu kafin babban zaben.

Kwamishinan ya ce hukumar ta yi wani taro da dukkan Kwamishinoninta ma Jihohi 36 da Abuja a ranar 28 ga watan Janairu.

Ya ce a yayin taron, hukumar ta karbi rahoto daga Kwamishinonin nata kan yanayin karbar katinan a Kananan Hukumomin Najeriya 774.

Idan za a iya tunawa, a yayin wani taro da Kwamishinonin hukumar, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sha alwashin cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da karin mutane sun sami damar karbar katinan nasu don yin zabe.

“Amma wadanda suka yi rijistar fiye da sau daya, kada ma su wahalar da kansu zuwa karbar katin, saboda ba mu buga nasu ba,” in ji Farfesa Mahmood.