✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

INEC ta sanya ranar fara rajistar zabe

Duk masu matsala za su iya gyarawa da zarar an bude shafin yin rajistar.

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da ranar 28 ga watan Yunin 2021 a matsayin ranar da za a fara rajistar katin zabe ta Intanet.

Kwamishinan Hukumar na Kasa Mai Kula da Wayar da Kan Jama’a, Mista Festus Okoye ne ya sanar da haka a ranar Juma’a a Dutse babban birnin jihar Jigawa, yayin shirye-shiryen zaben cike gurbin mazabar Gwaram da ke jihar.

  1. ’Yan bindiga sun harbe malamin Jami’ar Benin
  2. FGC Yauri: An kashe dan sanda, an sace malamai da dalibai

Ya ce, “INEC za ta bude shafin Intanet da mutane za su yi rajistar katin, daga bisani kuma sai su je ofishin jiharsu ko kananan hukumominsu, inda za a dauki hoton yatsunsu da hotunansu.

“Wanda kuma suke son sauya bayan wajen yin zabensu za su iya yi ta shafin Intanet din.

“Wanda kuma suka sami matsalar kati yayin zabe ko kuma ya kone duk za su iya gyarawa a shafin na Intanet,’’ cewar Mista Okoye.

Kwamishinan ya kuma ce nan gaba kadan shugaban hukumar na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu zai sanar da lokacin da za a fara rajistar katin ta zahiri.

Ya roki masu ruwa da tsaki a fadin Najeriya da su wayar da kan al’umma muhimmancin mallakar katin shaidar zabe.

Kazalika, ya yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen watsa labarai, da su sanar sa al’ummar muhimmancin yin rajistar katin ta kafar Intanet da zarar an fara. (NAN)