✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta soke rajistar zaben mutum miliyan 1.12

INEC ta jaddada cewa za ta fara rabon katunan zabe a watan Oktoban 2022

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke rajistar zaben mutum 1,126,359 daga cikin mutum 2,523,458 da suka yi rijista a karon farko daga watan yunin 2021 zuwa watan Janairun 2022.

Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kai, Festus Okoye, ne ya sanar da haka, kafin wayewar garin Talata a Abuja.

Ya jaddada cewa INEC za ta fara rabon katunan zaben mutanen da suka yi rajista a karon farko da wadanda suka sabunta nasu a watan Oktoba da watan Nuwamba masu kamawa.

Festus Okoye ya ce tun ranar 31 ga watan Yuni da aka rufe yin rijistar masu zabe hukumar ta fara aikin tatancewa da kuma tsaftace rajistar zabe.

“Da farko INEC ta sanar cewa an sami mutum 2,523,458 da suka yi rajistar zabe a karon farko daga ranar 28 ga watan Yuni, 2021,  zuwa  14 ga watan Janairu 2022.

“Sai dai kuma mutum 1,126,359 daga cikinsu rajistar da suka yi ba ta inganta ba, kuma an soke,” in ji Festus Okoye.

Hakan na nufin kawo yanzu karin mutum 1,397,099 aka samu a kan yawan masu zabe da ake da su a 2019 a Najeriya.

Okoye ya kara da cewa nan ba da jimawa ba hukumar za ta kammala aikin tantance wadanda suka yi rajistar zabe daga ranar 15 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Yuli, 2022, wadanda su ma a cikinsu aka gano mutane da yawa da suka yi rajista fiye da sau daya ko ba su cancanci yin rajista ba — kuma su ma an soka nasu.

Ya ce, “Wadanda hakan ta shafa sun hada da mutanen da suka saba ka’idojin hukumar, wadda ta ba da muhimmanci ga samun sahihin rajistar zabe domin tabbatar da gaskiya.

“Da zarar an kammala za a yi wa jama’a da bayani kamar yadda muka saba.

“Daga nan za a shigar da sabbin mutanen a tsohon rajistar da ake da ita, sannan a wallafa sunayen domin kowa ya gani, kamar yadda Sashe na19 (1) na Dokar Zabe ya 2022 ya tanada.”

Ya bayyana cewa hukumar na bin tsauraran matakai domin tabbatar da tsaftace rajistar da ke dauke da bayanan masu zabe.