✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Injin jirgin sama ya kama da wuta a sararin samaniya

Sai dai kamfanin ya ce dukkan fasinjojin jirgin sun sauka babu ko kwarzane

Fasinjojin wani jirgin sama da injin dinsa ya kama da wuta a sararin samaniya sun tsallake rijiya da baya.

Wuta ta tashi ne a injin jirgin saman na kamfanin Overland , wanda ya taso daga Ilori, babban birnin Jihar Kwara, yana dab da sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammaed da ke Legas.

Hatsarin dai ya faru ne da daren Laraba lokacin da daya daga cikin injinan jirgin ya kama da wuta yana dab da karasawa Legas.

Fasinjoji 33 ne dai a kan jirgin, kuma sun samu sauka a filin jirgin ba tare da wata matsala ba.

Rahotanni sun ce direban jirgin ne dai ya ankarar da hukumomin filin kan halin da ake ciki tun suna sama, inda suka yi gaggawar kawo masa dauki.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kamfanin jirgin na Overland ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce fasinjojin ba su wani ta da hankali ba sosai.

Kamfanin ya ce, “Overland na sanar da jama’a cewa jinginsa mai lamba OF1188, wanda ya tashi daga Ilorin zuwa Legas ya samu matsala a daya daga cikin injinansa [yau] Laraba, 15 Ga watan Yunin 2022, da misalin karfe 7:50 na yamma.

“Dukkan fasinjojin ciki 33 sun kasance a natse, sannan suka sauka lafiya, cikin bin matakan kariyar COVID-19, bayan jirgin ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

“Jirgin ya sauka ne a layin saukar jirage ma 18, bangaren dama, kuma babu fasinjan da ya ji ko da kwarzane,” inji kamfanin Overland.