✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB: An hallaka mutum 2 a hari kan ofishin ’yan sanda a Imo

Sai dai ’yan sanda sun hallaka biyu daga cikin maharan.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Imo ta ce matasa dauke da makamai sun tayar da bam a ofishin ’yan sanda na Njaba da ke Jihar inda suka lalata wani sashe na ginin.

Maharan dai mambobin haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ne ta IPOB ne.

To sai dai ’yan sandan sun sami nasarar kashe biyu daga cikinsu tare da kwace motarsu, yayin da sauran suka tsere.

Kakakin rundunar a Jihar, CSP Mike Abatam a cikin wata sanarwar ranar Asabar ya ce an kai harin ne da misalin karfe 1:20 na daren ranar Asabar amma aka tarwatsasu.

A cewar sanarwar, yayin da ake bincikar motar tasu da aka kwace, an sami bindiga kirar AK-47 da kuma harsasai guda 10 da wata karamar bindiga kirar gida da kuma wata jigida guda daya.

“Sun kuma kwance wani bam da suka dana a kusa da ofishin ’yan sanda na Njaba amma sun yi ’yar karamar barna,” inji sanarwar.

Kakakin ya kuma ce sun kaddamar da bincike a yankin domin kama maharan da suka tsere.