✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB: Mahara sun sake kone ofishin ‘yan sanda a Imo

Cikin kasa da sa’o’i 72 an kone ofisoshi hudu hudu a fadin jihar ta Imo.

Tashin-tashina da salwantar dukiyoyi na ci gaba da kamari a jihar Imo, duk da umarnin zaman gida da kungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB) ta yi a ranar Litinin.

Hakan dai bai hana wasu mahara kai hari tare da kone ofishin ’yan sanda na Amandugba da ke Karamar Hukumar Isu a jihar ba.

Wannan ya kawo adadin ofisoshin ’yan sandan da aka kone zuwa hudu cikin kasa da mako daya.

Rahotanni sun ce yayin da maharan suka isa bakin caji ofis din, sun banka wuta ciki, ba tare da bata lokaci ba.

Cikin wani faifan bidiyo da wakilinmu ya gani, ya ga yadda caji ofis din ke ci da wuta.

Tuni dai dokar zaman gidan da IPOB ta bayar ta jefa mutanen jihar ta Imo cikin dimuwa da shiga halin damuwa.

A cikin kasa da sa’o’i 72, mahara sun kone caji ofis din Atta da na Izombe da na Orji da na Isu da kuma kotun Majistare tare da cibiyar lafiya duk a jihar.

Sabon harin na zuwa ne sa’o’i 48 bayan kashe tsohon Hadimin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, wato Ahmed Gulak a jihar.

An kashe Gulak ne a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Sam Mbakwe da ke birnin Owerri a jihar, amma rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta yi nasarar kashe mutum shida da suka yi sanadin ajalinsa a ranar Lahadi.

Kazalika, an sake kashe jami’in hukumar shige da fice a jihar, Okiemutu Mrere a daren ranar Lahadi, a kan titin Owerri zuwa Fatakwal.

Da wakilin Aminiya ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan jihar Imo, Bala Elkana, ya ce ba shi da masaniya game da kone caji ofis din da maharan suka yi.