✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IPOB ta kai sabon hari ofishin ’yan sanda a Imo

Ana zargin mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB da kai harin na ranar Talata.

Rahotanni daga Jihar Imo sun ce a halin yanzu mahara da ake zargin ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun banka wa Babban Ofishin ’Yan Sanda na Orji, da ke Owerri wuta.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 12, inda aka yi ta musayar wuta da su, ko da yake babu cikakken bayani.

Harin na Owerri na zuwa ne awanni kadan bayan wasu da ake zargin ’yan IPOB ne sun kai hari a wani caji ofis inda suka kashe jami’an ’yan sanda a Jihar Enugu.

Maharan na Oghe a Jihar Enugu sun kuma kona ofishin ’yan sandan tare da cinna wa ababen hawan da ke harabarsa wuta.

Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da lamarin, sai dai bai yi karin bayani ba.