✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘IPOB’ ta kashe fitaccen malamin Musulunci a Kudu

Sheikh Ibrahim Iyiorji ya rasu a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke garin Abakaliki bayan harin

Mahara da ake zargi ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kashe fitaccen malamin Musulunci a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, Sheikh Ibrahim Iyiorji a gidansa da ke garin Abacha na Jihar Ebonyi.

A ranar Litinin Sheikh Ibrahim Iyiorji ya rasu a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke garin Abakaliki, inda aka kai shi domin samun kulawa.

Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURUC ta bukaci hukumomin Jihar ta Ebonyi da su tabbata sun kamo tare da hukunta duk masu hannu a kisa mashahurin malamin da aka yi a jihar.

A sakon ta’aziyyar MURIC ga gwamnati da al’ummar Jihar Ebonyi kan rasuwar, Shugaban kungiyar reshen Abuja, Sahuddeen Ustaz Yunus, ya ce, “Allah Ya bai wa gwamnatin jihar ikon gano duk abin da ke da alaka da kisan malamin da kuma daukar matakan da suka dace a kansu.

“Mu kuma, kowannenmu Allah Ya sa mu yi kyakkyawan karshe.”

Wakilinmu ya nemi karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Ebonyi, Chris Anyawu, domin samun karin bayani.

Sai dai jami’in ya shaida ba su da labarin kisan malamin da aka yi a garin Abacha.