✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB ta kashe mai ciki da wasu ’yan Arewa 11 a Anambra

Mai tsohon ciki da ’ya’yanta hudu da wasu ’yan Arewa shida IPOB ta yi wa kisan gilla.

Hankula sun tashi bayan ’yan ta’addan kungiyar a-waren IPOB sun kashe ’yan Arewa 12, ciki har da mace mai tsohon ciki da ’ya’yanta a Jihar Anambra.

Maharan na IPOB sun yi wa mai juna biyun da ’ya’yanta hudu da ’yan acaba biyar da wani mahauci, dukkansu ’yan Arewa, kisan gilla ne a yankin Isulo da ke Karamar Hukumar Orumba ta Arewa ta Jihar Anambra.

Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta yi zargin akwai shirin shafe ’yan Arewa mazauna yankin Kudu maso Gabashin Najeriya daga doron kasa a harin na ranar Lahadi.

Shugaban AYCF, Yerima Shettima, ya zargi Gwamnonin Kudu maso Gabas da hannu a kisan ’yan Arewa a yankin, saboda ba sa daukar matakai.

Don haka ya ce gwamnonin Kudu maso Yamma, “Wajibi ne ku kawo karshen yadda ake kashe ’yan Arewa da ba su bi ba, ba su gani ba, ko kuma ku fuskanci hukunci.

“Rashin hana kashe ’yan Arewa barkatai, da gwamnonin Kudu maso Gabas suka kasa a matsayinsu na shugabannin tsaron jihohinsu, ya nuna akwai wata makarkashiya ta shafe ’yan Arewa daga bankasa da sunan harin IPOB ko reshen kungiyar na ESN,” a cewarsa.

Ya kara da cewa ’yan Arewa ba za su lamunci dabi’ar auka wa ’yan uwansu mazauna ko masu gudanar da harkokinsu a yankin Kudu maso Gabas ba, kan abin da kai taka kara ya karya ba.

“Rashin maganar gwamnonin kan kisan gillar da aka yi wa ’yan uwanmu maza da mata a Kudu, dole ne a daina.

“Muna kuma jan kunne cewa babu wani dan Najeriya da ya fi wani iya rikici, saboda haka kada a yi kuskuren daukar yadda ’yan Arewa ke bin doka a matsayin kasawa.”

Tun ranar Lahadi wannan lamari ya faru, amma manyan kafofin yada labaran yankin ba su dauka ba, duk kuwa da yadda hotunan suka karade kafofin sada zumunta.

Aminiya ta bibiyi lamarin kisan gillan, wanda kungiyoyi da sauran masu rajin kare hakkin dan Adam da hukumomin tsaro sun yi tir da abin da suka kira munafincin manyan kafofin yada labarai, musamman na yankin Kudu, kan rashin daukar labarin.

Abin da ya faru

Sarkin Hausawan Karamar Hukumar Orunba ta Arewa, Alhaji Sa’id Muhammad, ya bayyana damuwa da cewa ’yan Arewa na shirin barin yankin Kudu maso Gabas saboda yadda reshen IPOB mai dauke da makami, ESN, ke yawan kashe musu ’yan uwa da makusanta.

Alhaji Sa’id Muhammad ya ce kisan da aka yi wa mai juna biyun da ’ya’yanta a yankin ba shi ne farau ba, domin an saba yi musu kisan rashin imani.

“Matar ’yar asalin Jihar Adamawa ce, wadda kafin rasuwarta take zaune a Orumba ta Kudu, ranar Lahadin ta ziyarci abokan zumuncinta tare da ’ya’yanta hudu.

“A hanyarsu ta komawa Orumba ta Kudu ne aka kashe su.

“Tana kan babur din wani dan acaba ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton bauna, suka kashe ta tare da ’ya’yanta hudu, amm adan acaban ya tsere,” inji shi.

Bidiyon kisan gillan da ya karade Twitter ya nuna mamatan kwance a cikin jini, an yi musu ruwan harsasai.

Hare-haren IPOB

IPOB ta yi wa ’yan Arewan kisan gilla ne bayan hare-haren da kungiyar take kaiwa kan kadarori da gine-gine da jami’an tsaro da jami’an gwamnati a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya a baya-bayan nan.

A ranar Asabar ne ta jefar da kan dan Majalisa Mai wakiltar mazabar gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, a majalisar dokokin jihar, wanda ta yi awon gaba da shi kimanin kwana shida kafin nan.

Kungiyar IPOB ta jima tana tayar da hankula tare da kashe jami’an tsaro da sauran jama’a a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, a yunkurinta na uzzura wa gwamnati domin ballewa daga Najeriya.