✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IPOB ta kashe ’yan Arewa 7 a Imo

'Yan ta'addar sun bude wuta kan mai uwa da wabi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta tabbatar da kisan wasu mutum bakwai da ake zargin ’yan ta’addan IPOB da aikatawa.

Kakakin rundunar a jihar, CSP Mike Abattam, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce, “A ranar 01/8/2022 da misalin karfe 11 na dare, jami’in dan sanda mai kula da hedkwatar Ogbaku a Owerri, jihar lmo, ya samu kiran waya cewar IPOB sun kai hari.

“Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) ce ta kai harin, inda mayakanta suka yi ta harbe-harbe a wani gini da ke Orogwe, karamar hukumar Owerri ta yamma, jihar Imo.”

Ya ce yayin harin, an kashe mutum bakwai, wasu kuma sun samu munanan raunuka.

Ya ce, “Jami’an ’yan sandan shiyyar sun yi gaggawar tattara mutanensu sannan suka bi bayan maharan.

“Tawagar ta yi gaggawar garzayawa da wadanda suka jikkata zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Owerri, sannan aka mika gawar wadanda suka mutu zuwa dakin ajiye gawarwaki.

“Abin takaici, jimillar mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a harin, yayin da wasu shida suka samu raunuka, kuma an garzaya da su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Owerri a Jihar Imo.

“Kwamishunan ’Yan Sandan jihar, CP Mohammed Ahmed Barde, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike a kan lamarin, inda ya yi alkawarin cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kama wadanda suka aikata wannan danyen aikin tare da fuskantar doka.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Sannan, ya yi kira da a kwantar da hankali, ya kuma umarci mutanen jihar da su taimaka wa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro ta hanyar ba su sahihin bayanai da kuma kai rahoton duk wani abu da ba su aminta da shi ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.”