✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB ta kulla kawance da ’yan tawayen Kamaru

Kawancen zai kunshi bayar da horo da musayar makamai tsakanin kungiyoyin biyu.

Haramtacciyar kungiyar na ta ’yan awaren Biyafara ta IPOB ta kulla wani kawance da ’yan tawayen kasar Kamaru da ke kokarin ballewa daga kasar, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar wa Aminiya.

Kawancen dai zai kunshi harkokin bayar da horo da kuma musayar makamai tsakanin kungiyoyin biyu.

Ko da yake har yanzu kawancen bai riga ya fito fili ba tukunna, bincike ya nuna ’yan tawayen na yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi a Kamaru masu son kafa kasar Ambazoniya kan shigo Najeriya cikin sauki ta Jihar Kuros Riba, saboda dadadden tarihi da al’adun yankunan biyu.

Yayin da IPOB ke yakar hukumomin Najeriya domin kafa kasar Biyafara, su kuwa ’yan tawayen na Kamaru na yaki ne ta kungiyoyin AWL da ADF domin ballewa daga kasar.

Rahotanni sun ce ana nuna damuwa matuka kan yuwuwar alakar karuwar hare-haren na IPOB da kuma kulla sabon kawancen.

A ranar 10 ga watan Afrilu 2021, Shugabancin ’yan awaren Kamarun na AWL ya sanar da cewa ya kulla kawance da ’yan IPOB a fafutukarsu ta cimma manufa daya.

Wani taron tattaunawa ta fasahar Zoom da aka dauka kuma aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna jagoran IPOB, Nnamdi Kanu da na AWL, Dokta Lucas Cho Ayaba, ya nuna yadda kungiyoyin suka amince su yi aiki tare.

Duka shugabannin biyu dai na jagorantar kungiyoyin ’yan tawayen ne daga kasashen waje.

“Yanzu mun fahimci abin da ke faruwa, za mu ci gaba da sa ido yadda ya kamata,” inji wani jami’in tsaro da bai amince a ambaci sunansa ba.

“Akwai alaka tsakaninsu saboda tsagerun Ambazoniya na bayar da horo ga takwarorinsu na IPOB,” inji wata majiyar.

Wani binciken manufofin kasashen ketare ya nuna cewa kungiyoyin biyu sun amince su yi aiki tare wajen tsare kan iyakoki, musayar makamai da kuma bayar da horo a tsakaninsu.

Yarjejeniyar IPOB da Ambazoniya

Yayin taron na Zoom dai na watan Afrilu, shugabannin kungiyoyin biyu sun amince su yi duk mai yuwuwa wajen jawo hankulan kasashen duniya domin su amince da fafutukarsu ta ballewa daga kasashen na Najeriya da Kamaru.

Sun ce mutanen yankunan biyu na fama da danniya da rashin ci gaba, wadanda mulkin mallaka ya kara ta’azzarawa.

Sun ce yunkurin nasu wani mataki ne na ceto ilahirin nahiyar Afirka daga mulkin danniya da zalunci.

Kanu ya ce “Tsawon shekaru, iyaye da kakanninmu sun jure irin cin kashin da ake musu cikin fatan cewa wata rana zai zama tarihi. Amma mun fahimci wadannan azzaluman ba za su taba barinmu mu numfasa ba.

“Hasali ma sai dada kara musu kaimu hakan ya yi. Wannan ne dalilin da ya sa Biyafara da Ambazoniya muka yanke shawarar yin aiki tare domin ceto yankunanmu masu tarihi mai kamanalceceniya.

“Ya zuwa yanzu, duk da cewar gwagwarmayarmu a wurare daban-daban take, amma fuska daya muka sa gaba. Muna so mu ceto Afirka kamar yadda ’yan kabilar Bantu suka yi.

“A ’yan kwanaki masu zuwa, za mu ci gaba da tuntubar juna a duk lokacin da bukatar hakan ta taso har sai mun kai ga gaci,” inji Kanu.

Shi kuwa da yake nasa jawabin, Dokta Ayaba ya ce yankunan na da dadadden tarihi kasancewar a da suma suna karkashin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ne, in banda a shekarar 1961 da suka gabatar da bukatar hadewa da yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi a Kamaru, a zauren Majalisar yankin da ke Enugu.

Ya ce, “Kamar yadda ka ce, mu mutane daya ne. Ina so in tabbatarwa ’yan Ambazoniya cewa mun karbi bukatarku hannu bibbiyu. Akwai bukatar ceto yankunanmu daga kowanne irin nau’i na danniya, kuma kawancen namu zai yi aiki ne a matakai guda uku.

“A cikin wannan lokacin, za mu wayar da kan jama’a sosai ta yadda kowacce yarjejeniya da za mu kulla za ta sami karbuwa a wurinsu,” inji Dokta Ayaba.

Bincike ya nuna cewa akwai ’yan asalin kasar Kamaru a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudancin Najeriya da dama wadanda ko dai suke zaune a yankunan, ko kuma suke zaman gudun hijira saboda rikicin da ya addabi kasarsu.

Sai dai babu wasu harkokin ayyukan ’yan tawayen na IPOB na zahiri da ke wakana tsakanin al’ummun kasashen biyu.